Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 2:2-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Sai aka faɗa wa Sarkin Yariko, aka ce, “Ga waɗansu mutane sun shigo nan da daddare domin su bincike ƙasar.”

3. Sarkin Yariko kuwa ya aika wurin Rahab ya ce, “Fito da mutanen da suka zo wurinki, waɗanda suka shiga gidanki, gama sun zo ne domin su leƙi asirin ƙasar duka.”

4. Amma macen ta riga ta ɓoye mutanen nan biyu, sai ta ce, “Gaskiya ce, mutanen sun zo wurina, amma ban san ko daga ina suka zo ba,

5. da maraice kuma, sa'ad da za a rufe ƙofar garin, sai mutanen suka fita, inda suka tafi kuwa ban sani ba, ku bi su da sauri, gama za ku ci musu.”

6. Gama ta riga ta kai su bisa rufin ɗaki, ta rufe su da ƙasheshen rama waɗanda ta shimfiɗa a bisa rufin.

7. Mutanen kuwa suka tafi don su bi bayansu a hanyar Urdun har zuwa mashigai. Da fitar masu bin sawun, sai aka rufe ƙofar garin.

8. Amma kafin 'yan leƙen asirin ƙasar su kwanta, sai ta tafi wurinsu a bisa rufin ɗakin,

9. ta ce musu, “Na sani Ubangiji ya ba ku ƙasar, tsoronku kuma ya kama mu har zukatan mazaunan ƙasar duka sun narke saboda ku.

10. Gama mun ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Bahar Maliya ya ƙafe a gabanku a sa'ad da kuka fito daga Masar, da irin abin da kuka yi wa sarakunan nan biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin Urdun, wato Sihon da Og, waɗanda kuka hallakar da su sarai.

11. Da muka ji, sai zukatanmu suka narke, har ba sauran ƙarfin hali da ya ragu a kowane mutum saboda ku. Gama Ubangiji Allahnku shi ne Allahn da yake a Sama daga bisa, da duniya a ƙasa.

12. Yanzu fa, ku rantse mini da Ubangiji, kamar yadda na yi muku alheri, haka ku kuma za ku yi wa gidan mahaifina, ku ba ni tabbatacciyar alama.

13. Ku ceci mahaifina, da mahaifiyata, da 'yan'uwana mata da maza, da dukan abin da yake nasu, ku ceci rayukanmu daga mutuwa.”

14. Mutanen kuwa suka ce mata, “Ranmu a bakin naki, idan ba ki tone al'amarinmu ba, za mu yi miki alheri da aminci sa'ad da Ubangiji ya ba mu ƙasar.”

15. Sa'an nan ta zurarar da su da igiya ta taga, gama gidanta yana haɗe da garun birnin ne.

16. Sai ta ce musu, “Tafi cikin tsaunuka domin kada masu bin sawun su same ku, ku ɓuya a wurin kwana uku, har masu bin sawun su komo, sa'an nan ku kama hanyarku.”

17. Mutanen suka ce mata, “Za mu kuɓuta daga rantsuwarki wadda kika rantsar da mu.

18. A lokacin da za mu shigo ƙasar, sai ki ɗaura wannan jan kirtani a tagar da kika zurarar da mu, ki kuma kawo mahaifinki, da mahaifiyarki, da 'yan'uwanki, da dukan iyalin gidan mahaifinki a gidanki.

19. Idan waninku ya fita daga ƙofar gidanki zuwa kan titi, to, alhakin jininsa yana bisa kansa, mu kuwa sai mu kuɓuta. Amma idan aka sa wa wani hannu wanda yake cikin gida tare da ke, alhakin jininsa yana kanmu.

Karanta cikakken babi Josh 2