Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 18:7-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Lawiyawa ba su da rabo tare da ku gama aikin Ubangiji shi ne rabonsu, da rabin ta Manassa sun riga sun sami nasu rabo wanda Musa, bawan Ubangiji, ya ba su a hayin gabashin Urdun.”

8. Joshuwa ya umarci mutanen da za su tafi su auna ƙasar, ya ce, “Ku shiga cikin ƙasar duka, ku auna sa'an nan ku komo wurina, ni kuwa zan jefa muku kuri'a a gaban Ubangiji a nan Shilo.”

9. Sai mutanen suka tafi, suka ratsa ƙasar tudu da ta gangare, suka auna ƙasar, suka raba ta kashi bakwai, suka lasafta garuruwan da suke ciki, sa'an nan suka koma wurin Joshuwa a Shilo.

10. Joshuwa kuwa ya jefa musu kuri'a a gaban Ubangiji a Shilo. Ta haka ya rarraba ƙasar ga jama'ar Isra'ila, kowa ya sami rabonsa.

11. Kuri'ar kabilar Biliyaminu bisa ga iyalanta ta fito. Yankin ƙasar da ya faɗo mata ke nan, ya zama a tsakanin yankin ƙasar kabilar Yahuza da na jama'ar Yusufu.

12. A wajen arewa iyakar ta tashi daga Urdun, ta bi ta tsaunin da yake arewa da Yariko, ta kuma haura tudu wajen yamma, har zuwa hamadar Bet-awen inda ta ƙare.

13. Daga can iyakar ta yi kudu, ta nufi cibiyar Luz, wato Betel, ta gangara zuwa Atarot-addar a bisa dutsen da yake kudu da Bet-horon ta kwari.

14. Daga nan iyakar ta nausa ta nufi yammacin kudancin dutse da yake kudu, daura da Bet-horon, sa'an nan ta tsaya a Kiriyat-ba'al, wato Kiriyat-yeyarim, birnin Yahuza. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma.

15. A wajen kudu kuwa iyakar ta fara daga karkarar Kiriyat-yeyarim, daga can ta miƙa zuwa Efron a maɓuɓɓugar ruwan Neftowa.

16. Iyakar kuma ta gangara zuwa gefen dutsen da yake fuskar kwarin ɗan Hinnon, wanda yake arewa wajen ƙarshen kwarin Refayawa. Ta kuma gangara zuwa kwarin Hinnom ta yi kudu daura da Yebusiyawa, ta gangara zuwa En-rogel.

17. Sai ta nausa ta yi wajen arewa zuwa En-shemesh, sa'an nan ta tafi Gelilot wanda yake daura da hawan Adummim. Daga nan ta gangara zuwa Dutsen Bohan, ɗan Ra'ubainu.

18. Sai ta wuce ta yi arewa daura da gefen Bet-araba, daga nan ta gangara zuwa Araba.

19. Ta kuma zarce zuwa arewa daura da gefen Bet-hogla, ta tsaya a arewacin gaɓar Tekun Gishiri a ƙarshen Urdun wajen kudu.

20. Kogin Urdun shi ne iyakar a wajen gabas. Waɗannan su ne iyakokin yankin ƙasar da iyalan kabilar Biliyaminu suka gāda.

21. Biranen iyalan kabilar Biliyaminu ke nan Yariko, da Bet-hogla, da Emekkeziz,

22. da Bet-araba, da Zemarayim, da Betel,

23. da Awwim, da Fara, da Ofra,

24. da Kefar-ammoni, da Ofni, da Geba. Birane goma sha biyu ke nan tare da ƙauyukansu.

25. Akwai kuma Gibeyon, da Rama, da Biyerot,

26. da Mizfa, da Kefira, da Moza,

Karanta cikakken babi Josh 18