Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 18:4-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ku ba ni mutum uku daga kowace kabila, ni kuwa in aike su, su auna ƙasar yadda za a raba ta gādo, sa'an nan su komo wurina.

5. Sai su raba ƙasar kashi bakwai. Kabilar Yahuza za ta ci gaba da zama a yankin ƙasarta a wajen kudu, mutanen gidan Yusufu kuwa su zauna a yankin ƙasarsu a wajen arewa.

6. Ku auna ƙasar, ku raba ta kashi bakwai, sa'an nan ku kawo mini taswirar ƙasar. Ni kuwa zan jefa muku kuri'a a gaban Ubangiji Allahnmu.

7. Lawiyawa ba su da rabo tare da ku gama aikin Ubangiji shi ne rabonsu, da rabin ta Manassa sun riga sun sami nasu rabo wanda Musa, bawan Ubangiji, ya ba su a hayin gabashin Urdun.”

8. Joshuwa ya umarci mutanen da za su tafi su auna ƙasar, ya ce, “Ku shiga cikin ƙasar duka, ku auna sa'an nan ku komo wurina, ni kuwa zan jefa muku kuri'a a gaban Ubangiji a nan Shilo.”

9. Sai mutanen suka tafi, suka ratsa ƙasar tudu da ta gangare, suka auna ƙasar, suka raba ta kashi bakwai, suka lasafta garuruwan da suke ciki, sa'an nan suka koma wurin Joshuwa a Shilo.

10. Joshuwa kuwa ya jefa musu kuri'a a gaban Ubangiji a Shilo. Ta haka ya rarraba ƙasar ga jama'ar Isra'ila, kowa ya sami rabonsa.

11. Kuri'ar kabilar Biliyaminu bisa ga iyalanta ta fito. Yankin ƙasar da ya faɗo mata ke nan, ya zama a tsakanin yankin ƙasar kabilar Yahuza da na jama'ar Yusufu.

12. A wajen arewa iyakar ta tashi daga Urdun, ta bi ta tsaunin da yake arewa da Yariko, ta kuma haura tudu wajen yamma, har zuwa hamadar Bet-awen inda ta ƙare.

13. Daga can iyakar ta yi kudu, ta nufi cibiyar Luz, wato Betel, ta gangara zuwa Atarot-addar a bisa dutsen da yake kudu da Bet-horon ta kwari.

14. Daga nan iyakar ta nausa ta nufi yammacin kudancin dutse da yake kudu, daura da Bet-horon, sa'an nan ta tsaya a Kiriyat-ba'al, wato Kiriyat-yeyarim, birnin Yahuza. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma.

Karanta cikakken babi Josh 18