Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 12:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Waɗannan su ne sarakunan ƙasar, waɗanda Isra'ilawa suka cinye da yaƙi, suka mallaki ƙasarsu a hayin Kogin Urdun daga yamma, tun daga kwarin Arnon har zuwa Dutsen Harmon da dukan Araba a wajen gabas,

2. Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda yake zaune a Heshbon, wanda yake mulki tun daga Arower wadda take iyakar kwarin Arnon, daga tsakiyar kwarin har zuwa Kogin Yabbok a iyakar Ammonawa,

3. daga kuma Araba zuwa gabashin Tekun Kinneret da zuwa Tekun Araga, wato Tekun Gishiri, a wajen gabas ta hanyar Ber-yeshimot, da wajen kudu zuwa gangaren gindin Dutsen Fisga,

4. da kuma Og, Sarkin Bashan, ɗaya daga cikin sauran Refayawa, wato gwarzayen nan waɗanda suka zauna a Ashtarot da Edirai.

5. Ya mallaki Dutsen Harmon, da Salka, da dukan Bashan, har zuwa iyakar Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa, da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon.

Karanta cikakken babi Josh 12