Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 63:6-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Da fushina na tattake dukan sauran al'umma, na farfashe su. Na kwararar da jinin ransu a ƙasa.”

7. Zan faɗi ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa,Zan yabe shi saboda dukan abin da ya yi mana.Ya sa wa jama'ar Isra'ila albarka mai yawa,Saboda jinƙansa da ƙaunarsa marar matuƙa.

8. Ubangiji ya ce, “Su mutanena ne, ba za su ruɗe ni ba.” Saboda haka kuwa ya cece su

9. daga dukan wahalar da suke sha. Ba mala'ika ne ya cece su ba, amma Ubangiji ne. Da ƙaunarsa da juyayinsa ya fanshe su. A koyaushe yake lura da su a dā,

10. amma suka i masa tayarwa, suka cika shi da ɓacin rai. Saboda haka Ubangiji ya yi gāba da su, ya kuwa yi yaƙi da su.

11. Amma suka tuna da zamanin dā, zamanin Musa bawan Ubangiji, suka yi tambaya suka ce, “Yanzu fa, ina Ubangiji yake wanda ya ceci shugabannin jama'arsa daga teku? Ina Ubangiji yake, wanda ya ba Musa iko musamman?

12. Ina Ubangiji yake wanda ya yi manyan al'amura da ikonsa ta wurin Musa, ya raba ruwan teku a gaban jama'arsa, domin ya yi wa kansa madawwamin suna?”

13. Sa'ad da Ubangiji ya bi da su ta ruwa mai zurfi, suka taka kamar ingarmun dawakai, ba su ko yi tuntuɓe ba.

14. Kamar yadda ake bi da shanu cikin kwari mai dausayi, haka Ubangiji ya ba mutanensa hutawa. Haka kuma Ubangiji ya bi da mutanensa, ya kuwa kawo ɗaukaka ga sunansa.

15. Ya Ubangiji, ka dube mu daga Sama, wurin da kake cike da tsarki da ɗaukaka. Ina kulawan nan da kake yi mana? Ina ikon nan naka? Ina ƙaunan nan taka da juyayin nan naka? Kada ka watsar da mu.

Karanta cikakken babi Ish 63