Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 60:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ki tashi, ya Urushalima, ki haskaka kamar rana,Daukakar Ubangiji tana haskakawa a kanki kamar rana!

2. Duhu zai rufe sauran al'umma,Amma hasken Ubangiji zai haskaka a kanki,Daukakarsa za ta kasance tare da ke!

3. Za a jawo al'ummai zuwa ga haskenki,Sarakuna kuma zuwa asubahin sabon yininki.

4. Ki duba kewaye da ke, ki ga abin da yake faruwa,Mutanenki suna ta tattaruwa domin su komo gida!'Ya'yanki maza za su taho daga nesa,Za a ɗauki 'ya'yanki mata kamar yara.

5. Za ki ga wannan, ki cika da farin ciki,Za ki yi rawar jiki saboda jin daɗi.Za a kawo miki dukiyar al'ummai,Wato waɗanda suke a ƙasashen hayi.

6. Babban ayarin raƙuma zai zo daga Madayana da Efa.Za su zo daga Sheba, su kawo zinariya da kayan ƙanshi.Mutane za su ba da labari mai daɗi a kan abin da Allah ya yi!

7. Dukan tumaki na Kedar da Nebayot,Za a kawo miki su hadaya,A kuwa miƙa su a kan bagade domin Ubangiji ya ji daɗi.Ubangiji zai darajanta Haikalinsa fiye da dā.

8. Waɗannan jiragen ruwa fa? Suna tafe kamar gizagizai,Kamar kurciyoyi suna komowa gida.

9. Jiragen ruwa ne suke zuwa daga manisantan ƙasashe,Suna kawo mutanen Allah gida.Suna tafe da azurfa da zinariya,Domin su girmama sunan Ubangiji,Allah Mai Tsarki na Isra'ila,Wanda ya sa dukan al'ummai su girmama mutanensa.

Karanta cikakken babi Ish 60