Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 54:10-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Duwatsu da tuddai za su ragargaje,Amma ƙaunar da nake yi miki ba za ta ƙare ba sam.Zan cika alkawarina na salama har abada.”Haka Ubangiji ya faɗa, shi wanda yake ƙaunarki.

11. Ubangiji ya ce,“Ya Urushalima, mai shan wahala, birnin da yake cikin halin ƙaƙa naka yi,Ba ki da wanda zai ta'azantar da ke.Zan sake gina harsashinki da duwatsu masu daraja.

12. Zan gina hasumiyarki da jan yakutu,Da ƙofofinki kuma da duwatsu masu haske kamar hasken wuta,Da garun da ya kewaye ki kuwa zan gina ta da lu'ulu'ai.

13. “Ni kaina zan koya wa mutanenki,Zan kuwa ba su wadata da salama.

14. Adalci da gaskiya za su ƙarfafa ki.Za ki tsira daga shan zalunci da razana.Gama ba za su kusace ki ba.

15. Idan wani ya far miki,Ya yi ne ba da yardata ba,Dukan wanda ya hau ki da yaƙi zai fāɗi!

16. “Ni ne na halicci maƙeriWanda ya zuga wuta ya kuwa ƙera makamai.Ni ne kuma na halicci mayaƙiWanda yakan mori makamai domin kisa.

17. Amma ba makamin da aka ƙera da ya isa ya cuce ki,Za ki iya amsa wa dukan waɗanda za su yi ƙararki.Zan kāre bayina,In kuwa ba su nasara.”Ubangiji ne ya faɗa.

Karanta cikakken babi Ish 54