Duwatsu da tuddai za su ragargaje,Amma ƙaunar da nake yi miki ba za ta ƙare ba sam.Zan cika alkawarina na salama har abada.”Haka Ubangiji ya faɗa, shi wanda yake ƙaunarki.