Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 5:1-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku saurara in raira muku wannan waƙa,Waƙar abokina da gonar inabinsa.Abokina yana da gonar inabiA wani tudu mai dausayi.

2. Ya kauce ƙasar ya tsintsince duwatsun,Ya daddasa itatuwan inabi mafi kyau.Ya gina hasumiya don a yi tsaronsu,Ya kuma haƙa rami inda za a matse 'ya'yan inabin.Ya yi ta jira don 'ya'yan inabin su nuna,Amma ko wannensu tsami take gare shi.

3. Saboda haka, abokina ya ce, “Ku jama'ar da yake zaune a Urushalima da Yahuza, ku shara'anta tsakanina da gonar inabina.

4. Akwai abin da ban yi mata ba? Me ya sa ta yi 'ya'yan inabi masu tsami, maimakon 'ya'yan inabi masu kyau da nake sa zuciya.

5. “Ga abin da zan yi wa gonar inabina. Zan cire shingen da yake kewaye da ita, in rushe bangon da ya kāre ta, in bar namomin jeji su cinye ta, su tattake ta.

6. Zan bar ciyayi su rufe ta. Ba zan yi wa kurangar inabin aski ba, ko in yi mata noma, amma zan bar sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa su rufe ta. Har ma zan sa gizagizai su hana ta ruwan sama.”

7. Isra'ila ita ce gonar inabin Ubangiji Mai Runduna,Jama'ar Yahuza su ne itatuwan inabin da aka daddasa.Ya sa zuciya za su yi abin da yake mai kyau,Amma a maimakon haka sai suka zama masu kisankai!Ya zaci za su aikata abin da yake daidai,Amma waɗanda suka fāɗa hannunsu kururuwa suke, suna neman adalci!

8. Kun shiga uku! Kuna ƙara wa kanku gidaje da gonaki a kan waɗanda kuke da su a dā. Ba da jimawa ba za a ga ba sauran filin da zai ragu ga kowa, ku kaɗai za ku zauna a ƙasar.

9. Na ji Ubangiji Mai Runduna yana cewa, “Duk waɗannan manya manyan gidaje kyawawa za su zama kangwaye.

10. Kadada biyar na gonar inabi za ta ba da kwalaba shida kaɗai na ruwan inabi. Garwa ashirin na iri za su ba da tsabar hatsi garwa biyu!”

11. Kun shiga uku! Kukan tashi da sassafe ku fara sha, ku yi ta sha har yamma ta yi sosai, ku raba dare kuna buguwa.

12. A cikin bukukuwanku kuna kaɗa garaya, da bandiri, da bushe-bushe, da ruwan inabi. Amma ba ku gane da abin da Ubangiji yake yi ba.

13. Don haka za a kwashe ku, ku zama 'yan sarƙa, a raba ku da ƙasarku. Yunwa za ta kashe shugabanninku, sauran jama'a kuwa ƙishirwa za ta kashe su.

14. Lahira ta ƙosa, ta wage bakinta. Ta lanƙwame manyan mutanen Urushalima da sauran babban taron jama'a masu hayaniya.

15. Za a kunyatar da kowa, dukan masu girmankai za a ƙasƙantar da su.

16. Amma Ubangiji Mai Runduna yana nuna girmansa ta wurin aikata abin da yake daidai, yana kuma bayyana shi Mai Tsarki ne, ta yadda yake shara'anta jama'arsa.

Karanta cikakken babi Ish 5