Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 45:11-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila,Shi wanda ya halicce su, ya ce,“Ba ka da iko ka yi mini tambaya game da 'ya'yana,Ko ka faɗa mini abin da ya kamata in yi!

12. Ni ne wanda ya halicci duniya,Na kuma halicci mutum don ya zauna cikinta.Da ikona na shimfiɗa sammai,Ina kuwa mallakar rana, da wata, da taurari.

13. Ni kaina na iza Sairus ya yi wani abu,Don ya cika nufina ya daidaita al'amura.Zan miƙar da kowace hanyar da zai yi tafiya a kai.Zai sāke gina birnina, wato Urushalima,Ya kuma 'yantar da mutanena da suke bautar talala.Ba wanda ya yi ijara da shi, ko ya ba shi rashawa don ya yi wannan.”Ubangiji Mai Runduna ne ya faɗi wannan.

14. Ubangiji ya ce wa Isra'ila,“Dukiyar Masar da ta Habasha za ta zama taku,Dogayen mutanen Seba kuma za su zama bayinku,Za su bi ku suna a ɗaure da sarƙoƙi.Za su rusuna a gabanku su tuba, su ce,‘Allah yana tare da ku, shi kaɗai ne Allah.’ ”

15. Allah na Isra'ila, wanda ya ceci mutanensa,Shi ne yakan ɓoye kansa.

16. Su waɗanda suka yi gumaka, dukansu za su sha kunya,Dukansu za su zama abin kunya.

17. Amma Ubangiji ya ceci Isra'ila,Nasararsa kuwa za ta tabbata har abada,Mutanensa ba za su taɓa shan kunya ba.

18. Ubangiji ne ya halicci sammai,Shi ne wanda yake Allah!Shi ne ya shata duniya ya kuma yi ta,Ya kafa ta, ta kahu da ƙarfi, za ta yi ƙarƙo!Bai halicce ta hamada da ba kome a ciki ba,Amma wurin zaman mutane.Shi ne wanda ya ce, “Ni ne Ubangiji,Ba kuwa wani Allah, sai ni.

Karanta cikakken babi Ish 45