Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 4:3-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Duk wanda aka rage a Urushalima, wanda Ubangiji ya nufa da rayuwa, za a ce da shi mai tsarki.

4. Ta wurin ikonsa Ubangiji zai shara'anta al'ummar, ya kuma tsarkake ta, ya wanke laifin Urushalima, har da na jinin da aka zubar a can.

5. Sa'an nan a kan Dutsen Sihiyona, da a kan dukan waɗanda suka tattaru a can, Ubangiji zai aika da girgije da rana, hayaƙi da hasken harshen wuta kuma da dare. Darajar Ubangiji za ta rufe, ta kuma kiyaye birnin duka.

Karanta cikakken babi Ish 4