Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 37:5-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sa'ad da Ishaya ya karɓi saƙon sarki Hezekiya,

6. sai ya aika masa da amsa cewa, “Ubangiji ya ce kada ka damu da irin zargin da Assuriyawa suke ta yi a kansa.

7. Ubangiji zai sa Sarkin Assuriya ya ji jita-jitar da za ta sa ya koma ƙasarsa, Ubangiji kuwa zai kashe shi a can.”

8. Shugaban mayaƙan Assuriya ya ji labari sarkin ya bar Lakish, yana can yana yaƙi da birnin Libna sai ya janye.

9. Sai Assuriyawa suka ji, cewa mayaƙan Masarawa, waɗanda sarki Tirhaka na Habasha take yi wa jagora, suna zuwa su far musu da yaƙi. Sa'ad da sarkin ya ji haka sai ya aika wa sarki Hezekiya da wasiƙa,

10. ya ce masa, “Allahn da kake dogara gare shi ya faɗa maka, ba za ka faɗa a hannuna ba, amma kada ka yarda wannan ya ruɗe ka.

11. Ka dai ji abin da Sarkin Assuriya ya yi wa duk ƙasar da ya yi niyyar hallakarwa. Kana tsammani za ka kuɓuta?

12. Kakannina sun hallakar da biranen Gozan, da Haran, da Rezef, suka kuma kashe mutanen Eden, mazaunan Telassar, ba ko ɗaya daga cikin gumakansu da ya iya cetonsu.

13. Ina sarakunan biranen Hamat da Arfad, da Sefarwayim, da Hena, da Iwwa?”

14. Sarki Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga hannun manzannin, ya karanta ta. Sa'an nan ya shiga Haikali, ya ajiye wasiƙar a gaban Ubangiji,

15. ya yi addu'a,

16. ya ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, kana kan kursiyinka, kai kaɗai ne Allah, kana mulkin dukan mulkokin duniya. Ka halicci duniya da sararin sama.

17. Yanzu, ya Ubangiji, ka ji mu, ka kuma dube mu. Ka kasa kunne ga dukan abubuwan da Senakerib yake ta faɗa, yana zaginka, ya Allah mai rai.

18. Dukanmu mun sani, ya Ubangiji, yadda sarakunan Assuriya suka hallakar da al'ummai masu yawa, suka mai da ƙasashensu kufai, marasa amfani,

19. suka ƙaƙƙone gumakansu waɗanda ba Allah ba ne ko kaɗan, siffofi ne kurum na itace da na dutse, da mutane suka yi da hannuwansu.

20. Yanzu dai, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga Assuriyawa domin dukan al'umman duniya su sani kai ne Allah kai kaɗai.”

21. Sa'an nan Ishaya ya aiki manzo zuwa wurin sarki Hezekiya, ya faɗa masa amsar Ubangiji a kan addu'ar sarki.

Karanta cikakken babi Ish 37