Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 37:16-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. ya ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, kana kan kursiyinka, kai kaɗai ne Allah, kana mulkin dukan mulkokin duniya. Ka halicci duniya da sararin sama.

17. Yanzu, ya Ubangiji, ka ji mu, ka kuma dube mu. Ka kasa kunne ga dukan abubuwan da Senakerib yake ta faɗa, yana zaginka, ya Allah mai rai.

18. Dukanmu mun sani, ya Ubangiji, yadda sarakunan Assuriya suka hallakar da al'ummai masu yawa, suka mai da ƙasashensu kufai, marasa amfani,

19. suka ƙaƙƙone gumakansu waɗanda ba Allah ba ne ko kaɗan, siffofi ne kurum na itace da na dutse, da mutane suka yi da hannuwansu.

20. Yanzu dai, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga Assuriyawa domin dukan al'umman duniya su sani kai ne Allah kai kaɗai.”

21. Sa'an nan Ishaya ya aiki manzo zuwa wurin sarki Hezekiya, ya faɗa masa amsar Ubangiji a kan addu'ar sarki.

22. Ubangiji ya ce, “Birnin Urushalima yana yi maka dariya, kai Sennakerib, yana kuma yi maka ba'a.

23. Wa kake tsammani kana raina, kana yi masa ba'a? Ba ka ba ni girma ba, ni Allah mai tsarki na Isra'ila.

24. Ka aike da barorinka don su yi mini fāriya, da cewa ka ci nasara da duwatsu mafi tsayi da karusanka, har da ƙwanƙolin Dutsen Lebanon. Kana fāriya da cewa a can ka sare dogayen itatuwan al'ul da na fir, ka kuma kai wuri mafi nisa na jeji.

25. Ka kuma yi fāriya da cewa ka haƙa rijiyoyi a baƙuwar ƙasa, ka kuma sha ruwansu, sojojinka kuma sun tattake Kogin Nilu da ƙafafunsu, har ya ƙafe.

26. “Ba ka taɓa sani, na riga na shirya a yi haka tuntuni ba? Yanzu ne kuwa na cika wannan. Ni na ba ka iko ka ragargaza birane masu kagarai su zama tsibin ɓuraguzai.

27. Mutanen da suke zaune a can marasa ƙarfi ne. Sun firgita, sun suma. Sun zama kamar ciyawa a saura, ko hakukuwan da suka tsiro a kan rufi, waɗanda zafin iskar gabas ta buga su.

28. “Amma na san kome game da kai, abin da kake yi da inda kake tafiya. Na san yadda ka harzuƙa gāba da ni.

Karanta cikakken babi Ish 37