Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 30:15-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya ce wa jama'a, “Ku komo gare ni a natse, ku dogara gare ni. Sa'an nan za ku zama ƙarfafa ku zauna lafiya.” Amma ba ku yarda ba!

16. A maimakon haka sai kuka shirya ku tsere wa maƙiyanku a kan dawakai masu gudu. Daidai ne, tilas ku tsere! Tsammani kuke saurin gudun dawakanku ya isa, amma waɗanda za su fafare ku sun fi ku gudu!

17. Dubunku za su gudu da ganin abokin gābanku ɗaya, abokan gāba biyar sun isa su sa dukanku ku gudu. Ba abin da zai ragu daga cikin rundunar sojojinku, sai sandan tutarku kaɗai da take kan tudu.

18. Duk da haka dai, Ubangiji yana jira ya yi muku alheri. A shirye yake ya yi muku jinƙai, domin a kullum yana aikata abin da yake daidai. Ta wurin dogara ga Ubangiji ake samun farin ciki.

19. Ku jama'ar da suke zaune a Urushalima ba za ku ƙara yin kuka ba. Ubangiji mai juyayi ne, sa'ad da kuka yi kuka gare shi neman taimako, zai amsa muku.

20. Ubangiji zai sa ku ku sha wahala, amma shi kansa zai kasance tare da ku, ya koya muku, ba za ku ƙara wahalar nemansa ba.

21. Idan kuka kauce daga hanya zuwa dama ko hagu, za ku ji muryarsa a bayanku yana cewa, “Ga hanyan nan, ku bi ta.”

22. Za ku kwashe gumakanku waɗanda aka dalaye da azurfa, da waɗanda aka rufe da zinariya, ku jefar da su kamar abin ƙyama, kuna ihu, kuna cewa, “Ku ɓace mana da gani!”

23. Duk lokacin da kuka shuka amfanin gonakinku, Ubangiji zai aiko da ruwan sama ya sa su girma, zai ba ku kaka mai albarka, shanunku kuma za su sami makiyaya wadatacciya.

24. Takarkaranku da jakunanku da suke huɗar gonakinku za su ci harawa mafi kyau duka.

25. A wannan rana sa'ad da aka kame kagaran abokan gābanku, aka kashe jama'arsu, rafuffukan ruwa za su malalo daga kowane tsauni da kowane tudu.

26. Wata zai yi haske kamar rana, hasken rana zai riɓanya har sau bakwai kamar a tattara hasken rana na kwana bakwai a maishe shi ɗaya! Dukan wannan zai faru sa'ad da Ubangiji zai ɗaure raunukan da ya yi musu, ya warkar da su.

27. Ana iya ganin ikon Allah da ɗaukakarsa daga nesa! Wuta da hayaƙi suna nuna fushinsa. Ya yi magana, maganarsa tana ƙuna kamar wuta.

Karanta cikakken babi Ish 30