Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 3:14-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Ubangiji ya kawo dattawa da shugabannin jama'arsa a gaban shari'a. Ga laifin da ya same su da shi, “Kun washe gonakin inabi, kun cika gidajenku da abin da kuka ƙwato daga matalauta.

15. Ba ku da izinin da za ku ragargaza jama'ata, ku cuci matalauta, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”

16. Ubangiji ya ce, “Duba irin girmankai da matan Urushalima suke da shi! Suna tafe suna hura hanci, a koyaushe suna ta fara'a irin ta yaudara, suna takawa ɗaya ɗaya a hankali da mundaye a ƙafafunsu, suna cas cas.

17. Amma zan hukunta su, in aske kawunansu, in bar su ƙwal.”

18. Rana tana zuwa sa'ad da Ubangiji zai raba matan Urushalima da dukan abin da suke taƙama da shi, da kayan adon da suke sawa a ƙafafunsu, da kawunansu, da wuyansu,

19. da hannuwansu. Zai raba su da lulluɓinsu,

20. da hulunansu. Zai raba su da layun da suke sa wa damatsansu, da kwankwasonsu,

21. da ƙawanen da suka sa a yatsotsinsu da hancinsu.

22. Ubangiji zai raba su da dukan kyawawan rigunansu na ado, da manyan rigunansu, da mayafansu, da jakunkunansu,

23. da rigunansu na yanga, da ƙyallayensu na lilin, da adikai, da gyale masu tsawo waɗanda suke sawa a kawunansu.

Karanta cikakken babi Ish 3