Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 29:2-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. sa'an nan Allah zai kawo wa birnin wanda ake ce da shi, “Bagaden Allah,” masifa. Za a yi kuka a yi kururuwa, birnin kansa za a maishe shi bagade inda za a ƙona hadayun ƙonawa!

3. Allah zai tasar wa birnin, ya kewaye shi da yaƙi.

4. Urushalima za ta zama kamar fatalwar da take ƙoƙarin yin magana daga ƙarƙashin ƙasa, guni yana fitowa daga turɓaya.

5. Ya Urushalima, dukan baƙin da suka auka miki da yaƙi za a hure su kamar yadda iska take hure ƙura, sojojinsu kuma masu firgitarwa za a hure su kamar yadda iska take hure tattaka. Farat ɗaya ba zato ba tsammani,

6. Ubangiji Mai Runduna zai cece ki da tsawar hadiri da girgizar ƙasa. Zai aiko da hadirin iska da gagarumar wuta.

7. Sa'an nan dukan sojojin sauran al'umman da suka fāɗa wa birni inda bagaden Allah yake da yaƙi, da dukan makamansu, da kayayyakin yaƙinsu, kome da kome za su shuɗe kamar mafarki, kamar tunanin dare.

8. Dukan al'ummai da suka tattaru don su yaƙi Urushalima, za su zama kamar mutum mayunwaci da ya yi mafarki yana cin abinci, ya farka yana a mayunwacinsa, kamar wanda yake mutuwa da ƙishi ya yi mafarki yana kwankwaɗar ruwa, ya farka da busasshen maƙogwaro.

9. Ku ci gaba da aikin wautarku! Ku ci gaba da makancewarku, ku yi ta zama a makance. Ku bugu ba tare da kun sha ruwan inabi ba! Ku yi ta tangaɗi, ba don kun sha ko ɗigon ruwan inabi ba!

10. Ubangiji ya sa ku ku yi gyangyaɗi ku yi barci mai nauyi. Annabawa ne ya kamata su zama idon jama'a, amma Allah ya rufe idanunsu.

11. Za a ɓoye muku ma'anar kowane annabci na cikin wahayi. Zai zama kamar naɗaɗɗen littafin da aka liƙe. Ko kun kai wa wanda ya iya karatu, don ya karanta muku, zai ce ba zai iya ba saboda a liƙe yake.

Karanta cikakken babi Ish 29