Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 24:17-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Ya jama'ar duniya, razana, da wushefe, da tarkuna suna jiranku.

18. Duk wanda ya yi ƙoƙarin tserewa daga razana zai fāɗa cikin wushefe, wanda kuma ya tsere daga wushefe za a kama shi a tarko. Za a kwararo ruwa daga sama kamar da bakin ƙwarya, harsashin ginin duniya zai jijjigu.

19. Duniya za ta tsage, ta farfashe ta wage.

20. Duniya kanta za ta yi tangaɗi kamar mashayi, ta yi ta yin lau kamar rumfa a lokacin hadiri. Nauyin zunuban duniya ya rinjaye ta har ƙasa, za ta fāɗi, ba za ta ƙara tashi ba.

21. A wannan rana Ubangiji zai hukunta wa ikoki na sama, da sarakunan da suke a duniya.

22. Allah zai tattara sarakuna wuri ɗaya kamar ɗaurarru a rami, zai kulle su a kurkuku kafin lokacin da zai hukunta su ya yi.

23. Wata zai duhunta, rana ba za ta ƙara haskakawa ba, domin Ubangiji Mai Runduna yake sarauta. Zai yi mulki a Urushalima a kan Dutsen Sihiyona, shugabannin jama'a za su dubi ɗaukakarsa.

Karanta cikakken babi Ish 24