Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 24:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji zai hallaka duniya ya bar ta kufai. Zai kaɓantar da duniya ya watsar da jama'ar da take cikinta.

2. Bala'i ɗaya ne zai sami kowa da kowa, firistoci da sauran jama'a, bayi da iyayengijinsu, masu saye da masu sayarwa, masu ba da rance da masu karɓa, attajirai da matalauta.

3. Duniya za ta ragargaje ta zama kufai. Ubangiji ne ya faɗa, haka kuwa za a yi.

4. Duniya za ta bushe ta ƙeƙashe, duniya duka za ta raunana, duniya da sararin sama za su ruɓe.

5. Jama'ar sun ƙazantar da duniya da suka keta dokokin Allah, suka ta da alkawarin da ya yi don ya dawwama.

6. Saboda haka Allah ya aiko da la'ana ta hallaka duniya. Jama'arta suna karɓar sakayyar abin da suka aikata. 'Yan kalilan ne suka ragu da rai.

7. Kurangun inabi sun bushe, ruwan inabi ya yi kaɗan. Dukan wanda yake farin ciki a dā, yanzu sai baƙin ciki yake yi,

8. kaɗe-kaɗen garayunsu da gangunansu na farin ciki sun ƙare.

9. Babu sauran waƙar farin ciki ga mashayan ruwan inabi, ba kuma wanda zai ƙara jin daɗin ɗanɗanar ruwan inabi.

10. A cikin birni kome ya birkice, an kulle kowane gida don a hana mutane shiga.

11. Mutane za su tsaya a tituna, suna ihu, suna neman ruwan inabi. Farin ciki ya ƙare har abada, ya ƙare a ƙasar.

12. Birnin ya zama kango, an farfashe ƙofofinsa.

13. Wannan shi ne abin da zai sami kowace al'umma ko'ina a duniya. Zai zama kamar ƙarshen kaka sa'ad da aka karkaɗe zaitun daga kowane itace, aka kuma gama tsinke 'ya'yan inabi daga kurangar inabi.

14. Waɗanda suka tsira za su raira waƙa don farin ciki. Waɗanda suke wajen yamma za su ba da labarin girman Allah,

15. waɗanda suke wajen gabas kuma za su yabe shi. Jama'ar da take zaune a gefen teku za su yabi Ubangiji, Allah na Isra'ila.

Karanta cikakken babi Ish 24