Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 16:6-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Mutanen Yahuza sun ce, “Mun ji irin fāriyar da mutanen Mowab suke yi. Mun sani su masu girmankai ne, masu ruba, amma fankamarsu ta banza ce.”

7. Mutanen Mowab za su yi kuka saboda wahalar da suke sha. Dukansu za su yi kuka sa'ad da suka tuna da kyakkyawan abincin da suka riƙa ci a birnin Kir-hareset. Za a kore su har su fid da zuciya.

8. Gonakin da suke kusa da Heshbon, da gonakin inabin da suke Sibma an lalatar da su, gonakin inabin nan waɗanda ruwan inabinsu suke sa masu mulkin al'ummai su bugu. Da kurangunsu sun taɓa yaɗuwa zuwa gabas har suka kai birnin Yazar da cikin hamada, wajen yamma kuma sai da suka dangana da gefen Tekun Gishiri.

9. Yanzu ina kuka saboda gonakin inabin Sibma kamar yadda na yi wa na Yazar. Na zub da hawayena saboda Heshbon da Eleyale, domin ba a sami kaka mai albarka ba, wadda za ta sa mutane yin murna.

10. Ba wanda yake farin ciki a cikin sauruka masu dausayi. Ba wanda yake sowa ko waƙa a cikin gonakin inabi. Ba mai matse ruwan inabi, sowar murna ta ƙare.

11. Na yi nishi da ɓacin zuciya a kan Mowab, na yi nishi da baƙin ciki saboda Kir-heres.

12. Mutanen Mowab sun gajiyar da kansu da zuwa wurin matsafarsu na kan dutse da masujadarsu, suna addu'a, amma ba zai amfana musu kome ba.

13. Wannan shi ne jawabin da Ubangiji ya riga ya yi a kan Mowab.

14. Yanzu Ubangiji ya ce, “A shekara uku daidai, dukiyar Mowab mai yawan nan za ta ƙare. Daga cikin ɗumbun mutanenta 'yan kaɗan ne kaɗai za su ragu, za su kuma zama marasa ƙarfi.”

Karanta cikakken babi Ish 16