Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 14:15-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Amma a maimakon haka an saukar da kai a sashe mafi zurfi a lahira.

16. Matattu za su zura maka ido su yi mamaki. Za su yi tambaya su ce, “Ashe, ba wannan mutum ba ne ya girgiza duniya, ya sa mulkoki suka jijjigu?

17. Wannan shi ne wanda ya hallaka birane, ya mai da duniya hamada, wanda bai taɓa sakin ɗaurarru ko ya bar su su koma gida ba?”

18. Dukan sarakunan duniya suna kwance a cikin manya manyan kaburburansu,

19. amma kai ba ka sami kabari ba, jefar da gawarka aka yi don ta ruɓe. Aka hautsuna gawarka da gawawwakin mayaƙan da aka kashe cikin yaƙi. Tare da su aka jefa ka gangaren dutse, aka tattake.

20. Ba za a binne ka kamar sauran sarakuna ba, saboda ka lalata da ƙasarka, ka karkashe mutanenka. Daga cikin mugayen iyalinka ba wanda zai ragu.

21. A fara yanyanka su! 'Ya'ya maza na sarkin nan za su mutu saboda zunuban kakanninsu. Daga cikinsu ba wanda zai taɓa mallakar duniya, ko ya cika ta da birane.

22. Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan fāɗa wa Babila da yaƙi, in lalata ta, ba abin da zan bari, ko yara, ba wanda zai ragu. Ni, Ubangiji, na faɗi wannan.

23. Zan su Babila ta zama fadama, mujiyoyi za su zauna a can. Zan kuwa share Babila da tsintsiyar da za ta share kome. Ni, Ubangiji Mai Runduna, na faɗa.”

24. Ubangiji Mai Runduna ya rantse, ya ce, “Abin da na riga na shirya, haka zai faru. Abin da na yi niyyar yi, za a yi.

25. Zan hallaka Assuriyawa a ƙasata ta Isra'ila, in tattake su a kan duwatsuna. Zan 'yantar da jama'ata daga karkiyar Assuriyawa, daga nauyin da suka tilasta musu su ɗauka.

26. Abin da na shirya zan yi wa duniya, shi ne in miƙa hannuna domin in hukunta wa al'ummai.”

27. Ubangiji Mai Runduna ne ya ƙudura ya yi wannan, ya miƙa dantsensa don ya yi hukunci, ba kuwa mai iya hana shi.

28. Wannan shi ne jawabin da aka yi shelarsa a shekarar da sarki Ahaz ya rasu.

29. Ku mutanen Filistiya, sandan da ake dūkanku da shi ya karye, amma kada wannan ya zamar muku dalilin murna. Gama idan wani maciji ya mutu, wani mafi mugunta zai maye gurbinsa. Ƙwan maciji yake ƙyanƙyashe maciji mai tashi sama!

30. Ubangiji zai zama makiyayin jama'arsa wadda take talauce, zai kuma sa su zauna lafiya. Amma ku Filistiyawa, zai aukar muku da matsananciyar yunwa, wadda ba za ta bar ko ɗayanku da rai ba.

31. Ku yi kururuwa, ku yi kuka na neman taimako, dukanku biranen Filistiya! Ku razana dukanku! Ƙurar da ta murtuke tana zuwa daga arewa, mayaƙa ne, ba kuwa matsorata a cikinsu.

32. Ƙaƙa za mu amsa wa manzannin da suka zo gare mu daga Filistiya? Za mu faɗa musu, cewa Ubangiji ya tabbatar da Sihiyona, jama'arsa da suke shan wahala kuwa za su sami zaman lafiya a can.

Karanta cikakken babi Ish 14