Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 7:5-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. “ ‘Idan dai kun gyara hanyoyinku, da ayyukanku bisa kan gaskiya, idan da gaskiya kuke aikata adalci ga junanku,

6. idan ba ku tsananta wa baƙo, ko maraya, ko gwauruwa, wato matar da mijinta ya rasu, idan ba ku zubar da jinin marar laifi a wannan wuri ba, idan kuma ba ku bi abin da zai cuce ku ba, wato gumaka,

7. sa'an nan zan bar ku ku zauna a wannan wuri, a ƙasa wadda tuni na ba kakanninku har abada.

8. “ ‘Ga shi, kun amince da maganganu na ruɗami, marasa amfani.

9. Za ku yi ta yin sata, da kisankai, da zina, da rantsuwar ƙarya, da ƙona wa Ba'al turare, da bin waɗansu gumakan da ba ku sani ba?

10. Sa'an nan za ku zo ku tsaya a gabana a wannan Haikali, wanda ake kira da sunana, ku ce, “An cece mu,” don kawai ku ci gaba da yin dukan waɗannan abubuwan banƙyama?

11. Wannan Haikali wanda ake kira da sunana ya zama kogon mafasa a idanunku. Ga shi, ni da kaina na gani.’ ” in ji Ubangiji.

12. “ ‘Ku tafi Shilo wurin da na fara zaunar da sunana, ku ga abin da na yi mata saboda muguntar mutanena Isra'ila.

13. Yanzu kuwa saboda kun aikata waɗannan al'amura, sa'ad da na yi ta yi muku magana, amma ba ku kasa kunne ba, sa'ad da na kira ku, ba ku amsa ba,

14. domin haka zan yi wa Haikali wanda ake kira da sunana, wanda kuma kuka amince da shi, da kuma wurin da na ba ku, ku da kakanninku, kamar yadda na yi wa Shilo.

15. Zan kore ku daga gabana kamar yadda na yi wa dukan 'yan'uwanku, dukan zuriyar Ifraimu.’ ”

16. “Kai kuwa, Irmiya kada ka yi wa mutanen nan addu'a. Kada ka yi kuka ko addu'a dominsu, kada ka roƙe ni, gama ba zan ji ka ba.

17. Ba ka ga abin da suke yi a biranen Yahuza da titunan Urushalima ba?

18. Yara sukan tara itace, iyaye maza sukan haɗa wuta, iyaye mata sukan kwaɓa ƙullu don su yi wa gunkin nan wadda ake kira sarauniyar sama, waina. Sukan kuma miƙa wa gumaka hadayu na sha domin su tsokane ni.”

19. In ji Ubangiji, “Ni suke tsokana? Ashe, ba kansu ba ne don su ruɗar da kansu?”

20. Saboda haka ga abin da Ubangiji Allah ya ce, “Duba, zan kwarara fushina da hasalata a kan wannan wuri, a kan mutum duk da dabba, da akan itatuwan saura da amfanin gona. Zai yi ta cin wuta, ba kuwa za a kashe ba.”

21. Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Ku ba da hadayunku na ƙonawa da na sadakarku, ku ci naman.

22. A ranar da na fito da kakanninku daga ƙasar Masar, ban yi magana da su, ko na umarce su, a kan hadayun ƙonawa da na sadaka ba.

23. Amma na umarce su su yi biyayya da maganata, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena, su bi dukan al'amuran da na umarce su, domin lafiyarsu, don su zama lafiya.

24. Amma ba su yi biyayya ba, ba su kuma kula ba. Sai suka bi shawarar kansu da ta tattaurar muguwar zuciyarsu. Suka koma baya maimakon su yi gaba.

Karanta cikakken babi Irm 7