Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 7:15-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Zan kore ku daga gabana kamar yadda na yi wa dukan 'yan'uwanku, dukan zuriyar Ifraimu.’ ”

16. “Kai kuwa, Irmiya kada ka yi wa mutanen nan addu'a. Kada ka yi kuka ko addu'a dominsu, kada ka roƙe ni, gama ba zan ji ka ba.

17. Ba ka ga abin da suke yi a biranen Yahuza da titunan Urushalima ba?

18. Yara sukan tara itace, iyaye maza sukan haɗa wuta, iyaye mata sukan kwaɓa ƙullu don su yi wa gunkin nan wadda ake kira sarauniyar sama, waina. Sukan kuma miƙa wa gumaka hadayu na sha domin su tsokane ni.”

19. In ji Ubangiji, “Ni suke tsokana? Ashe, ba kansu ba ne don su ruɗar da kansu?”

20. Saboda haka ga abin da Ubangiji Allah ya ce, “Duba, zan kwarara fushina da hasalata a kan wannan wuri, a kan mutum duk da dabba, da akan itatuwan saura da amfanin gona. Zai yi ta cin wuta, ba kuwa za a kashe ba.”

21. Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Ku ba da hadayunku na ƙonawa da na sadakarku, ku ci naman.

22. A ranar da na fito da kakanninku daga ƙasar Masar, ban yi magana da su, ko na umarce su, a kan hadayun ƙonawa da na sadaka ba.

23. Amma na umarce su su yi biyayya da maganata, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena, su bi dukan al'amuran da na umarce su, domin lafiyarsu, don su zama lafiya.

24. Amma ba su yi biyayya ba, ba su kuma kula ba. Sai suka bi shawarar kansu da ta tattaurar muguwar zuciyarsu. Suka koma baya maimakon su yi gaba.

25. Tun daga ran da kakanninku suka fito ƙasar Masar, har zuwa yau na yi ta aika musu da dukan bayina annabawa kowace rana.

26. Duk da haka ba su saurare ni ba, ba su kula su ji ba, sai suka taurare zukatansu suka aikata mugun abu fiye da na kakanninsu.

Karanta cikakken babi Irm 7