Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 50:10-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Za a washe Kaldiyawa,Waɗanda suka washe su kuwa za suƙoshi,Ni Ubangiji na faɗa.

11. “Saboda kuna murna, kuna farinciki,Ku da kuka washe gādona,Saboda kuma kuna tsalle kamarkarsana a cikin ciyawa,Kuna haniniya kamar ingarmu,

12. Domin haka za a kunyatar da Babilasosai, inda kuka fito.Za ta zama ta baya duka a cikinsauran al'umma,Za ta zama hamada, busasshiyarƙasa.

13. Saboda fushin Ubangiji, ba wandazai zauna a cikinta,Za ta zama kufai,Duk wanda ya bi ta wajen Babila, zaiji tsoro,Zai kuma yi tsaki sabodalalacewarta.

14. “Dukanku 'yan baka, ku ja dāga, kukewaye Babila,Ku harbe ta, kada ku rage kibanku,Gama ta yi wa Ubangiji zunubi.

15. Ku kewaye ta da kuwwar yaƙi!Ta ba da gari,Ginshiƙanta sun fāɗi.An rushe garunta,Gama wannan sakayya ce taUbangiji.Ku sāka mata, ku yi mata kamaryadda ta yi.

16. Ku datse wa Babila mai shuka,Da mai yanka da lauje a lokacingirbi.Saboda takobin azzalumi,Kowa zai koma wurin mutanensa,Kowa kuma zai gudu zuwaƙasarsa.”

17. “Isra'ilawa kamar tumaki ne waɗanda zakuna suka bi su suna kora. Da farko dai Sarkin Assuriya ne ya cinye su. Yanzu kuwa Sarkin Babila, wato Nebukadnezzar, shi ne yake gaigayi ƙasusuwansu.

18. Saboda haka ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila na ce, zan yi wa Sarkin Babila da ƙasarsa hukunci, kamar yadda na hukunta Sarkin Assuriya.

Karanta cikakken babi Irm 50