Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 5:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. “Don me zan gafarce ki?'Ya'yanki sun rabu da ni,Sun yi rantsuwa da gumaka,Na ciyar da su har sun ƙoshi sosai,Suka yi karuwanci, suka ɗungumazuwa gidajen karuwai,

8. Kamar ƙosassun ingarmu suke,masu jaraba,Kowa yana haniniya, yana nemanmatar maƙwabcinsa.

9. Ba zan hore su saboda waɗannanabubuwa ba?Ni Ubangiji na ce, ba zan ɗauka wakaina fansa a kan wannanal'umma ba?

10. Ku haura, ku lalatar da gonarkurangar inabinta,Amma kada ku yi mata ƙarƙaf,Ku sassare rassanta,Gama su ba na Ubangiji ba ne.

11. Gama mutanen Isra'ila da mutanenYahuzaSun zama marasa aminci a gare ni.Ni Ubangiji na faɗa.”

12. Sun yi ƙarya a kan Ubangiji,Suka ce, “Ba abin da zai yi,Ba wata masifa da za ta same mu.Ba kuwa za mu ga takobi ko yunwaba.

13. Annabawa holoƙo ne kawai,Maganar ba ta cikinsu.Haka za a yi da su!”

14. Saboda haka Ubangiji Allah MaiRunduna ya ce,“Domin sun hurta wannan magana,Ga shi, zan sa maganata a bakinka tazama wuta,Waɗannan mutane kuwa su zamaitace,Wutar za ta cinye su.

15. “Ya ku mutanen Isra'ila, ga shi, inakawo mukuWata al'umma daga nesa,” in jiUbangiji,“Al'umma ce mai ƙarfin hali ta tunzamanin dā.Al'umma wadda ba ku san harshentaba,Ba za ku fahimci abin da suke faɗaba.

16. Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabarine,Dukansu jarumawa ne.

17. Za su cinye amfanin gonakinku daabincinku.Za su ƙare 'ya'yanku mata da maza.Za su cinye garkunanku na tumaki,da na awaki, da na shanu,Za su kuma cinye 'ya'yan inabinkuda na ɓaurenku.Za su hallaka biranenku masu kagarada takobi, waɗanda kuke fariya dasu.

Karanta cikakken babi Irm 5