Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 42:13-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. “Amma idan kuka ce ba za ku zauna a wannan ƙasa ba, kuka ƙi yin biyayya da muryar Ubangiji Allahnku,

14. kuna cewa, ‘Mun ƙi, mu, ƙasar Masar za mu tafi, inda ba za mu ga yaƙi ba, ba za mu ji ƙarar ƙahon yaƙi ba, yunwa kuma ba za ta same mu ba, a can za mu zauna.’

15. To, sai ku ji maganar Ubangiji, ya ku sauran mutanen Yahuza, Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, ‘Idan zuwa Masar kuka sa gaba don ku tafi ku zauna a can,

16. to, takobin nan da kuke jin tsoro, zai ci muku can a ƙasar Masar, yunwan nan kuma da kuke jin tsoro za ta bi ku zuwa Masar ta tsananta muku, a can za ku mutu.

17. Duk waɗanda suka sa gaba zuwa Masar domin su zauna can, da takobi, da yunwa, da annoba su ne ajalinsu. Ba wanda zai ragu, ba wanda zai tsira daga masifar da zan aukar musu.’

18. “Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa'ad da kuka tafi Masar. Za ku zama najasa, da abin ƙyama, da la'ana, da abin ba'a. Wannan wuri kuwa ba za ku ƙara ganinsa ba.’

19. “Ya ku sauran mutanen Yahuza, Ubangiji ya ce, ‘Kada ku tafi Masar.’ Ku tabbata fa na faɗakar da ku yau,

20. cewa in kun ratse, to, a bakin ranku. Gama kun aike ni wurin Ubangiji Allah cewa, ‘Ka roƙar mana Ubangiji Allahnmu. Dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya ce ka faɗa mana kuma za mu aikata.’

21. A wannan rana kuwa na faɗa muku abin da ya ce, amma ba ku yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku a kan kowane abin da ya aiko ni in faɗa muku ba.

Karanta cikakken babi Irm 42