Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 41:11-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Amma sa'ad da Yohenan ɗan Kareya, tare da dukan shugabannin sojoji da suke tare da shi suka ji irin wannan mugun aiki wanda Isma'ilu ɗan Netaniya ya yi,

12. sai suka kwashe mutanensu duka, suka tafi su yi yaƙi da Isma'ilu ɗan Netaniya. Suka iske shi a babban tafkin da take a Gibeyon.

13. Sa'ad da dukan jama'ar da Isma'ilu ya kwashe suka ga Yohenan ɗan Kareya, da dukan shugabannin sojoji tare da shi, sai suka yi murna.

14. Dukan mutanen nan da Isma'ilu ya kwashe su ganima daga Mizfa, suka juya, suka koma wurin Yohenan ɗan Kareya.

15. Amma Isma'ilu ɗan Netaniya tare da mutum takwas suka tsere suka gudu zuwa wurin Ammonawa.

16. Sai Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji da suke tare da shi, suka kwashe dukan sauran jama'a, waɗanda Isma'ilu ɗan Netaniya ya kamo daga Mizfa bayan ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wato sojoji da mata, da yara, da bābāni, su ne Yohenan ya komo da su daga Gibeyon.

17. Suka fa tafi suka zauna a wurin Kimham kusa da Baitalami. Suna nufin su tafi Masar,

Karanta cikakken babi Irm 41