Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 41:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A watan bakwai sai Isma'ilu ɗan Netaniya, ɗan Elishama, na cikin zuriyar sarauta, ɗaya daga cikin ma'aikatan sarki, ya zo a wurin Gedaliya ɗan Ahikam a Mizfa tare da mutum goma. Sa'ad da suke cin abinci tare a Mizfa,

2. Isma'ilu ɗan Netaniya, da mutanen nan goma da take tare da shi, suka tashi suka sare Gedaliya ɗan Ahikam ɗan shafan, da takobi, suka kashe shi, wato Gedaliya wanda Sarkin Babila ya naɗa ya zama mai mulkin ƙasar.

3. Isma'ilu kuma ya kashe dukan Yahudawa da suke tare da Gedaliya a Mizfa da waɗansu sojojin Kaldiyawa da suke a wurin.

4. Kashegari bayan da an kashe Gedaliya, tun kafin wani ya sani,

5. sai waɗansu mutane, su tamanin, suka zo daga Shekem, da Shilo, da Samariya, da gemunsu a aske, da tufafinsu a kece, da jikunansu a tsage. Suka kawo hadaya ta gari da hadayar turare domin su miƙa a Haikalin Ubangiji.

6. Sai Isma'ilu ɗan Netaniya ya fito daga cikin Mizfa yana kuka, don ya tarye su. Da ya sadu da su, sai ya ce musu, “Ku zo mu tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam!”

7. Sa'ad da suka shiga birnin, sai Isma'ila ɗan Nataniya da mutanen da suke tare da shi suka kashe su, suka jefa su a wata rijiya.

8. Amma waɗansu mutum goma daga cikinsu suka ce wa Isma'ila, “Kada ka kashe mu, gama muna da rumbunan alkama, da na sha'ir, da kuma man zaitun da zuma a ɓoye a cikin gonaki.” Sai ya bar su, bai kashe su tare da abokansu ba.

Karanta cikakken babi Irm 41