Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 4:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce,“Ya mutanen Isra'ila, idan za kujuyo ku komo wurina,Idan kuka kawar da abubuwanbanƙyama daga gabana,Kuka kuma bar yin shakka,

2. Idan kun yi rantsuwa kuka ce,‘Har da ran Ubangiji kuwa,‘Da gaskiya, da aminci, da adalci,Sa'an nan sauran al'umma za su soin sa musu albarka,Za su kuma yabe ni.”

3. Ubangiji ya ce wa mutanen Yahuza da na Urushalima,“Ku kafce saurukanku,Kada ku yi shuka cikin ƙayayuwa.

4. Ya ku mutanen Yahuza da naUrushalima,Ku yi wa kanku kaciya dominUbangiji,Ku kawar da loɓar zukatankuDon kada fushina ya fito kamarwuta,Ya cinye, ba mai iya kashewa,Saboda mugayen ayyukan da kukaaikata.”

5. “Ku yi shela a cikin Yahuza,Ku ta da murya a Urushalima, kuce,‘Ku busa ƙaho a dukan ƙasar!’Ku ta da murya da ƙarfi, ku ce,‘Ku tattaru, mu shiga birane masugaru.’

6. Ku ta da tuta wajen Sihiyona!Ku sheƙa a guje neman mafaka,kada ku tsaya!Gama zan kawo masifa da babbarhalaka daga arewa.

7. Zaki ya hauro daga cikinruƙuƙinsa,Mai hallaka al'ummai ya kamahanya,Ya fito daga wurin zamansa don yamai da ƙasarku kufai,Ya lalatar da biranenku, su zamakango, ba kowa.

8. Domin haka sai ku sa tufafinmakoki,Ku yi makoki ku yi kuka,Gama fushin Ubangiji bai rabu damu ba.”

9. Ubangiji ya ce, “A ranan nan, sarki da sarakuna, za su rasa ƙarfin hali, firistoci za su firgita, annabawa kuwa za su yi mamaki.”

Karanta cikakken babi Irm 4