Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 34:6-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Sai annabi Irmiya ya faɗa wa Zadakiya, Sarkin Yahuza, dukan maganan nan a Urushalima,

7. sa'ad da sojojin Sarkin Babila suke yaƙi da Urushalima da kuma dukan biranen da suka ragu na Yahuza, wato Lakish da Azeka. Waɗannan su kaɗai ne biranen Yahuza masu garu da suka ragu.

8. Ubangiji kuma ya yi magana da Irmiya bayan da Zadakiya ya yi alkawari da dukan mutanen Urushalima don a yi musu shelar ba da 'yanci,

9. cewa kowa ya saki bayinsa, mata da maza, waɗanda suke Yahudawa. Kada kowa ya riƙe bawa wanda yake Bayahude, ɗan'uwansa.

10. Sai suka yi biyayya. Dukan sarakuna da dukan jama'a waɗanda suka yi alkawarin, cewa kowa zai 'yantar da bawansa ko baiwarsa, ba za su ƙara bautar da su ba, suka yi biyayya, suka 'yantar da su.

11. Daga baya kuwa suka sāke komo da waɗannan bayi, mata da maza waɗanda suka 'yantar, suka kuma mai da su bayi.

12. Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce,

13. “Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari da kakanninku lokacin da na fito da su daga ƙasar Masar daga bauta, na ce,

14. ‘A shekara ta bakwai, dole ne ku 'yantar da 'yan'uwanku, Ibraniyawa, waɗanda aka sayar muku, suka kuwa bauta muku shekara shida. Dole ne ku 'yantar da su daga bautarku.’ Amma kakanninku ba su kasa kunne gare ni ba.

Karanta cikakken babi Irm 34