Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 32:3-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Zadakiya Sarkin Yahuza, ya sa shi a kurkuku, gama ya ce, “Don me kake yin annabci? Ka ce, Ubangiji ya ce, ga shi, zai ba da wannan birni a hannun Sarkin Babila, zai kuwa cinye shi da yaƙi.

4. Zadakiya Sarkin Yahuza kuwa, ba zai tsere wa Kaldiyawa ba, amma za a ba da shi a hannun Sarkin Babila. Zai yi magana da shi fuska da fuska, ya kuma gan shi ido da ido.

5. Sarkin Babila kuwa zai tafi da Zadakiya zuwa Babila. Zai zauna can sai lokacin da na ziyarce shi. Ko da ya yi yaƙi da Kaldiyawa ba zai yi nasara ba.”

6. Irmiya ya ce, “Ubangiji ya yi magana da ni, cewa

7. ga shi, Hanamel, ɗan Shallum kawuna, zai zo wurina ya ce mini, ‘Ka sayi gonata wadda take a Anatot, gama kai ne ka cancanci ka fanshe ta, sai ka saye ta.’ ”

8. Sai Hanamel ɗan kawuna ya zo wurina a gidan waƙafi, bisa ga faɗar Ubangiji, ya ce mini, “Ka sayi gonata wadda take a Anatot a ƙasar Biliyaminu, gama kai ne ka cancanta ka mallake ta, kai ne za ka fanshe ta, sai ka saye ta.” Sa'an nan na sani wannan maganar Ubangiji ce.

9. Sai na sayi gonar a Anatot daga hannun Hanamel ɗan kawuna, na biya shi shekel goma sha bakwai na azurfa.

10. Na sa hannu a takarda, na buga hatimi na liƙe, na sami shaidu na kuwa auna kuɗin da ma'auni.

11. Na ɗauki takardun ciniki waɗanda aka rubuta sharuɗan a ciki da wadda aka liƙe da wadda ba a liƙe ba,

12. na ba Baruk, ɗan Neriya, ɗan Ma'aseya, a gaban Hanamel, ɗan kawuna, da gaban shaidun da suka sa hannun a takardar shaidar sayen, da gaban dukan Yahudawa waɗanda suke zaune a gidan waƙafi.

13. Sai na umarci Baruk a gabansu cewa,

14. “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, ‘Ka ɗauki waɗannan takardun shaida, wadda aka liƙe da wadda ba a liƙe ba, ka sa su a cikin tukunyar ƙasa domin kada su lalace.’

15. Gama haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗa, ‘Gidaje, da gonaki, da gonakin inabi, za a sāke sayensu a ƙasan nan.’ ”

Karanta cikakken babi Irm 32