Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 32:24-44 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. “Ga shi, Kaldiyawa sun gina mahaurai kewaye da birnin da suka kewaye shi da yaƙi. Saboda takobi, da yunwa, da annoba aka ba da birnin a hannun Kaldiyawa, waɗanda suke yaƙi da birnin. Abin da ka faɗa ya tabbata, ka kuwa gani.

25. Duk da haka ya Ubangiji Allah, ka ce mini, ‘Sayi gonar da kuɗi, a gaban shaidu, ko da yake an ba da birnin a hannun Kaldiyawa.’ ”

26. Ubangiji kuwa ya ce wa Irmiya,

27. “Ni ne Ubangiji Allah na dukan 'yan adam, ba abin da ya fi ƙarfina.

28. Saboda haka, ni Ubangiji, na ce zan ba da wannan birni a hannun Kaldiyawa da hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, za su ci birnin.

29. Kaldiyawa da suke yaƙi da wannan birni za su zo, za su ƙone wannan birni da wuta ƙurmus, da gidaje waɗanda aka ƙona turare ga Ba'al a kan rufinsu. Aka kuma miƙa hadayu na sha ga gumaka, don su tsokane ni in yi fushi.

30. Gama jama'ar Isra'ila da ta Yahuza, tun daga ƙuruciyarsu, ba su aikata kome a gabana ba sai mugunta, ba abin da jama'ar Isra'ila suka yi, sai tsokanata da gumaka don in yi fushi da ayyukan hannuwansu, ni Ubangiji na faɗa.

31. Wannan birni ya tsokane ni ƙwarai tun lokacin da aka gina shi har zuwa yau, domin haka zan kawar da shi daga gabana.

32. Wannan kuwa saboda muguntar jama'ar Isra'ila ce da ta Yahuza, wadda suka yi don su tsokane ni in yi fushi, su da sarakunansu, da shugabanninsu, da firistocinsu, da annabawansu, da mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima.

33. Sun juya mini baya, ba su fuskance ni ba, ko da yake na yi ta koya musu, amma ba su saurara ga koyarwata ba.

34. Sun kafa gumakansu na banƙyama a cikin Haikalina wanda ake kira da sunana, sun kuwa ƙazantar da shi.

35. Sun gina wa Ba'al masujadai a kwarin ɗan Hinnom don su miƙa 'ya'yansu mata da maza hadaya ga Molek, ni kuwa ban umarce su ba, ba shi kuwa a tunanina. Ga shi, sun aikata wannan abin banƙyama, don su sa Yahuza ta yi zunubi.”

36. “Domin haka ga abin da ni Ubangiji Allah na Isra'ila na ce a kan wannan birni wanda ka ce, ‘An ba da shi ga Sarkin Babila, da takobi, da yunwa, da annoba.’

37. Ga shi, zan tattaro su daga dukan ƙasashe inda na kora su, da fushina, da hasalata, da haushina. Zan komo da su a wannan wuri, zan sa su su zauna lafiya.

38. Za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu.

39. Zan ba su zuciya ɗaya, da tafarki ɗaya domin su yi tsorona har abada, domin amfanin kansu da na 'ya'yansu a bayansu.

40. Zan yi madawwamin alkawari da su, ba zan fasa nuna musu alheri ba, zan kuwa sa tsorona a zukatansu domin kada su bar bina.

41. Zan ji daɗin yi musu alheri. Zan dasa su a wannan ƙasa da aminci da zuciya ɗaya.”

42. Gama haka Ubangiji ya faɗa, “Daidai kamar yadda na kawo wannan babbar masifa a kan jama'an nan, haka kuma zan kawo musu dukan waɗannan alherai da na alkawarta musu.

43. Za a sayi gonaki a wannan ƙasa wadda kake cewa ta zama kufai, ba mutum, ba dabba a ciki, wadda aka ba da ita ga Kaldiyawa.

44. Za a sayi gonaki da kuɗi, a sa hannu a kan sharuɗa, a hatimce su a gaban shaidu, a ƙasar Biliyaminu da wuraren da suke kewaye da Urushalima, da cikin garuruwan Yahuza, da na garuruwan ƙasar tudu, da a garuruwan kwaruruka, da a garuruwan Negeb, gama zan komar wa mutane da wadatarsu a ƙasarsu, ni Ubangiji na faɗa.”

Karanta cikakken babi Irm 32