Ga shi, zan tattaro su daga dukan ƙasashe inda na kora su, da fushina, da hasalata, da haushina. Zan komo da su a wannan wuri, zan sa su su zauna lafiya.