Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 30:18-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ubangiji ya ce,“Ga shi, zan komar wa alfarwarYakubu arzikinta,Zan kuma nuna wa wuraren zamansajinƙai,Za a sāke gina birnin a kufansa,Fādar kuma za ta kasance a indatake a dā.

19. Daga cikinsu za a ji waƙoƙin godiya.Da muryoyin masu murna.Zai riɓaɓɓanya su, ba za su zamakaɗan ba,Zan kuwa ɗaukaka su, ba za aƙasƙantar da su ba.

20. 'Ya'yansu za su zama kamar dā,Jama'arsu kuma za su kahu agabana,Zan hukunta dukan waɗanda sukazalunce su.

21. Sarkinsu zai zama ɗaya dagacikinsu,Mai mulkinsu kuma zai fito dagacikinsu.Zan kawo shi kusa, zai kuwa kusaceni,Gama wane ne zai yi ƙarfin hali yakusace ni? Ni Ubangiji na faɗa.

22. Za ku zama mutanena,Ni kuwa zan zama Allahnku.”

23. Ga hadirin hasalar Ubangiji ya taso,wato iskar guguwa,Zai huce a kan mugaye.

24. Zafin fushin Ubangiji ba zai huce ba,Sai ya aikata, ya kammala abubuwanda ya yi niyya a tunaninsa.A nan gaba mutanensa za su fahimciwannan.

Karanta cikakken babi Irm 30