Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 30:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce,

2. “Ni Ubangiji Allah na Isra'ila na ce, ‘Ka rubuta dukan maganar da na faɗa maka a littafi.

3. Gama kwanaki suna zuwa sa'ad da zan komo da mutanena, wato Isra'ila da Yahuza. Zan komo da su zuwa ƙasar da na ba kakanninsu, za su kuwa mallake ta,’ ni Ubangiji na faɗa.”

4. Waɗannan ne maganar da Ubangiji ya faɗa a kan Isra'ila da Yahuza.

5. “Ni Ubangiji na ce,Mun ji kukan gigitacce,Kukan firgita ba kuma salama.

6. Yanzu ku tambaya, ku ji,Namiji ya taɓa haihuwa?To, me ya sa nake ganin kowanenamiji yana riƙe da kwankwaso,Kamar mace mai naƙuda,Fuskar kowa kuma ta yi yaushi?

7. Kaito, gama wannan babbar rana ce,Ba kuma kamarta,Lokaci ne na wahala ga Yakubu,Duk da haka za a cece shi dagacikinta.”

8. Ubangiji Mai Runduna ya ce, “A wannan rana zan karya karkiya da take a wuyansu, in cire musu ƙangi, ba kuma za su ƙara zama bayin baƙi ba.

9. Amma za su bauta mini, ni Ubangiji Allahnsu, da Dawuda sarkinsu, wanda zan tayar musu da shi.”

10. Ubangiji ya ce,“Kada ka ji tsoro, ya baranaYakubu,Kada kuma ka yi fargaba, yaIsra'ila,Gama zan cece ka daga ƙasa mainisa,Zan kuma ceci zuriyarka daga ƙasarbautarsu.Yakubu zai komo, ya yi zamansa raia kwance,Ba kuwa za a tsoratar da shi ba.

11. Gama ina tare da kai don in cece ka,Zan hallaka dukan al'ummai sarai,Inda na warwatsa ku.Amma ku ba zan hallaka ku ba,Zan hore ku da adalci,Ba yadda za a yi in ƙyale ku bahukunci,Ni Ubangiji na faɗa.”

Karanta cikakken babi Irm 30