Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 26:8-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sa'ad da Irmiya ya gama faɗar dukan abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa wa dukan jama'a, sai firistoci, da annabawa, da dukan jama'a suka kama shi, suna cewa, “Mutuwa za ka yi!

9. Don me ka yi annabci da sunan Ubangiji, ka ce wannan Haikali zai zama kamar Shilo, wannan birni kuma zai zama kufai, ba mazauna a ciki?” Sai jama'a duk suka taru, suka kewaye Irmiya cikin Haikalin Ubangiji.

10. Sa'ad da sarakunan Yahuza suka ji waɗannan al'amura, sai suka fito daga gidan sarki zuwa Haikalin Ubangiji, suka zauna a bakin Sabuwar Ƙofa ta Haikalin Ubangiji.

11. Sai firistoci da annabawa suka faɗa wa sarakunan nan da jama'a duka, suka ce, “Mutumin nan ya cancanci hukuncin kisa, gama ya yi annabci gāba da wannan birni kamar yadda kuka ji da kunnuwanku.”

12. Sa'an nan sai Irmiya ya yi magana da dukan sarakuna da dukan jama'a, ya ce, “Ubangiji ne ya aiko ni in yi annabci gāba da wannan Haikali da wannan birni, da irin maganar da kuka ji.

13. Saboda haka yanzu sai ku gyara al'amuranku da ayyukanku, ku yi biyayya kuma da muryar Ubangiji Allahnku. Ubangiji kuwa zai janye masifar da ya hurta gāba da ku.

14. Amma ni kaina kuwa a hannunku nake, sai ku yi mini yadda kuka ga ya yi kyau, ya kuma dace a gare ku.

15. Ku tabbata dai, idan kuka kashe ni, za ku jawo hakkin jinin marar laifi a kanku da a kan wannan birni da mazauna a cikinsa, gama a gaskiya Ubangiji ne ya aiko ni wurinku domin in faɗa muku dukan maganan nan a kunnuwanku.”

16. Sarakuna kuwa da dukan jama'a suka ce wa firistoci da annabawa, “Wannan mutum bai yi abin da ya isa hukuncin kisa ba, gama ya yi magana da sunan Ubangiji Allahnmu.”

17. Sai waɗansu daga cikin dattawan ƙasar suka miƙe tsaye, suka ce wa dukan taron jama'a,

18. “Mika kuwa, mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya faɗa wa dukan mutanen Yahuza cewa,‘Ga abin da Ubangiji Mai Rundunaya ce,Za a nome Sihiyona kamar gona,Urushalima kuwa za ta zama tsibinjuji,Ƙwanƙolin dutsen Haikalin zai zamakurmi.’

19. Ashe, Hezekiya Sarkin Yahuza da dukan Yahuza sun kashe shi ne? Ashe, Hezekiya bai ji tsoron Ubangiji, ya roƙi alherinsa ba? Ashe, Ubangiji bai janye masifar da ya hurta a kansu ba? Yanzu fa gab muke da mu jawo wa kanmu babbar masifa.”

Karanta cikakken babi Irm 26