Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 26:2-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. “Ka tsaya a filin Haikalin Ubangiji, ka yi wa dukan biranen Yahuza magana, su waɗanda suka zo Haikalin Ubangiji domin su yi sujada. Ka faɗa musu dukan maganar da na umarce ka, kada ka rage ko ɗaya.

3. Mai yiwuwa ne su ji, har kowa ya juyo ya bar muguwar hanyarsa. Ni ma sai in janye masifar da na yi niyyar aukar musu da ita, saboda mugayen ayyukansu.”

4. Ubangiji ya faɗa wa Irmiya ya ce wa jama'a, “Haka Ubangiji ya ce, idan ba za ku kasa kunne gare ni ba, ku yi tafiya a dokata wadda na sa a gabanku ba,

5. ku kuma kula da zantuttukan bayina, annabawa, waɗanda na yi ta aiko muku, to, amma ba ku kula ba.

6. Saboda haka zan mai da wannan Haikali kamar Shilo, in mai da wannan birni ya zama abin la'ana ga dukan al'umman duniya.”

7. Firistoci, da annabawa, da dukan jama'a sun ji dukan maganan nan da Irmiya ya faɗa a cikin Haikalin Ubangiji.

8. Sa'ad da Irmiya ya gama faɗar dukan abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa wa dukan jama'a, sai firistoci, da annabawa, da dukan jama'a suka kama shi, suna cewa, “Mutuwa za ka yi!

9. Don me ka yi annabci da sunan Ubangiji, ka ce wannan Haikali zai zama kamar Shilo, wannan birni kuma zai zama kufai, ba mazauna a ciki?” Sai jama'a duk suka taru, suka kewaye Irmiya cikin Haikalin Ubangiji.

10. Sa'ad da sarakunan Yahuza suka ji waɗannan al'amura, sai suka fito daga gidan sarki zuwa Haikalin Ubangiji, suka zauna a bakin Sabuwar Ƙofa ta Haikalin Ubangiji.

11. Sai firistoci da annabawa suka faɗa wa sarakunan nan da jama'a duka, suka ce, “Mutumin nan ya cancanci hukuncin kisa, gama ya yi annabci gāba da wannan birni kamar yadda kuka ji da kunnuwanku.”

12. Sa'an nan sai Irmiya ya yi magana da dukan sarakuna da dukan jama'a, ya ce, “Ubangiji ne ya aiko ni in yi annabci gāba da wannan Haikali da wannan birni, da irin maganar da kuka ji.

Karanta cikakken babi Irm 26