Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 20:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Duk lokacin da zan yi magana,Nakan ta da murya in yi magana daƙarfi cewa,‘Hargitsi da hallakarwa!’Gama saboda maganar Ubangiji nazama abin zargi,Da abin ba'a dukan yini.

9. Idan na ce, ‘Ba zan ambaci Ubangijiba,Ban zan ƙara yin magana da sunansaba,’Sai in ji damuwa a zuciyata,An kulle ta a ƙasusuwana,Na gaji da danne ta a cikina,Ba zan iya jurewa ba.

10. Na ji mutane da yawa suna sa minilaƙabi cewa,‘Razana ta kowace fuska,’Suna cewa, ‘Mu la'anta shi!Mu la'anta shi!’Har ma da abokaina shaƙiƙaiSuna jira su ga fāɗuwata.Suka ce, ‘Watakila a ruɗe shi,Sa'an nan ma iya rinjayarsaMu ɗauki fansa a kansa.’

11. Amma Ubangiji kana tare da niKamar jarumi mai bantsoro,Don haka masu tsananta mini za suyi tuntuɓe,Ba za su rinjaye ni ba.Za su sha kunya ƙwarai,Gama ba za su yi nasara ba.Ba za a manta da su ba.

12. Ya Ubangiji Mai Runduna, maigwada adali,Mai ganin zuciya duk da tunani,Ka sa in ga sakayyar da za ka yimusu,Gama a gare ka nake kawoƙarata.”

13. Ku raira waƙa ga Ubangiji!Ku yabi Ubangiji!Gama ya kuɓutar da ran mabukacidaga hannun mugaye.

14. La'ananniya ce ranar da aka haifeni,Kada ranar da uwata ta haife ni ta yialbarka!

15. La'ananne ne mutum da ya kai wamahaifina labariCewa, “An haifa maka ɗa,” don yasa shi farin ciki.

16. Bari wannan mutum ya zama kamarbiranen da Ubangiji ya kaɓantarba tausayi.Bari ya ji kuka da safe,Da rana kuma ya ji gangamin yaƙi,

17. Domin bai kashe ni tun ina ciki ba.Da ma cikin uwata ya zama minikabari,In yi ta kwanciya a ciki har abada.

18. Me ya sa na fito daga cikin mahaifa,Don in ga wahala da baƙin ciki,Don kwanakin raina su ƙare dakunya?

Karanta cikakken babi Irm 20