Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 14:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Maganar da Ubangiji ya yi wa Irmiya a kan fari ke nan,

2. “Yahuza tana makoki,Ƙofofin biranenta suna lalacewa,Mutanenta suna kwance a ƙasa,suna makoki,Urushalima tana kuka da babbarmurya.

3. Manyan mutanenta sun aikibarorinsu su ɗebo ruwa.Da suka je maɓuɓɓuga, sai sukatarar ba ruwa.Sai suka koma da tulunansuhaka nan,An kunyatar da su, an ƙasƙantarda su,Suka lulluɓe kansu don kunya.

4. Saboda ƙasar ta bushe,Tun da ba a yi ruwa a kanta ba,Manoma sun sha kunya,Suka lulluɓe kansu don kunya.

5. Barewa ma a saura takan gudu,Ta bar ɗanta sabon haihuwa,Domin ba ciyawa.

6. Jakunan jeji suna tsaye a kan tuddanda ba ciyawa,Suna haki kamar diloli,Idanunsu ba su ganiDomin ba abinci.”

7. Irmiya ya ce,“Ko da yake zunubanmu su neshaidunmu,Ya Ubangiji, ka yi taimako sabodasunanka!Gama kāsawarmu ta yi yawa,Domin mun yi maka zunubi.

8. Ya kai, wanda kake begen Isra'ila,Mai Cetonta a lokacin wahala,Ƙaƙa ka zama kamar baƙo a ƙasar?Kamar matafiyi wanda ya kafaalfarwarsa a gefen hanya don yakwana, ya wuce?

9. Ƙaƙa ka zama kamar wanda bai sanabin da zai yi ba,Kamar jarumin da ya kasa yinceto?Duk da haka, ya Ubangiji, kana nana tsakiyarmu.Da sunanka ake kiranmu,Kada ka bar mu!”

10. Haka Ubangiji ya ce a kan waɗannan mutane, “Sun cika son yawaceyawace, ba su iya zama wuri ɗaya, don haka ni Ubangiji, ban yarda da su ba, zan tuna da laifofinsu in hukunta zunubansu.”

Karanta cikakken babi Irm 14