Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Hab 2:13-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ba Ubangiji Mai Runduna ne ya sa mutanen duniya, su yi wahala, wuta ta cinye ba?Sun kuma gajiyar da kansu a banza?

14. Duniya za ta cika da sanin ɗaukakar Ubangiji,Kamar yadda ruwa ya cika teku.

15. “Taka ta ƙare, kai wanda yake sa maƙwabtanka su sha,Kana zuba musu dafinka har su bugu,Don ka dubi tsiraicinsu!

16. A maimakon daraja, za ka sha ƙasƙanci.Ka sha kai da kanka, ka yi tangaɗi.Ƙoƙon da yake a hannun Ubangiji zai faɗo a kanka,Kunya za ta rufe darajarka.

17. Ɓarnar da aka yi wa Lebanon za ta komo kanka,Ka kashe dabbobinta, yanzu dabbobi za su tsorata ka,Saboda jinin mutanen da ka zubar,Da wulakancin da ka yi wa duniya,Da birane, da mazauna a cikinsu.

18. “Ina amfanin gunki sa'ad da mai yinsa ya siffata shi?Shi siffa ne da aka yi da ƙarfe, mai koyar da ƙarya.Gama mai yinsa yakan dogara ga abin da ya siffata,Sa'ad da ya yi bebayen gumaka.

19. Tasa ta ƙare, shi wanda ya ce da abin da aka yi da itace, ‘Farka!’Ya kuma ce wa dutse wanda ba ya ji, ‘Tashi!’Wannan zai iya koyarwa?Ga shi, an dalaye shi da zinariya da azurfa,Ba ya numfashi ko kaɗan.

20. “Amma Ubangiji yana cikin tsattsarkan Haikalinsa,Bari duniya ta yi tsit a gabansa.”

Karanta cikakken babi Hab 2