Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 9:22-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama don a yi ƙanƙara a bisa mutum da dabba da bisa dukan itatuwan saura a dukan ƙasar Masar.”

23. Sai Musa ya miƙa sandansa sama, Ubangiji kuwa ya aiko da tsawa da ƙanƙara, wuta kuwa ta bi ƙasar. Ubangiji ya sa aka yi ƙanƙara a bisa ƙasar Masar.

24. Ƙanƙarar tana faɗowa, wuta kuma tana tartsatsi a cikin ƙanƙara. Aka yi ƙanƙara mai tsananin gaske irin wadda ba a taɓa yi ba cikin dukan ƙasar Masar tun lokacin da ta zama al'umma.

25. Ƙanƙarar ta bugi ko'ina a Masar. Dukan abin da yake cikin saura, mutum duk da dabba, da tsire-tsire duka, ƙanƙara ta buge su. Duk itatuwan da yake a saura aka ragargaza su.

26. Sai dai a ƙasar Goshen inda Isra'ilawa suke, ba a yi ƙanƙara ba.

27. Fir'auna ya aika, aka kirawo Musa da Haruna, ya ce musu, “Lalle a wannan karo na yi laifi, Ubangiji shi ne da gaskiya. Ni da jama'ata muke da kuskure.

28. Ku roƙi Ubangiji ya tsai da tsawar da ƙanƙarar. Ni kuwa na yi alkawari zan bar ku ku tafi, ba za ku ƙara tsayawa a nan ba.”

29. Musa ya ce masa, “Da fitata daga cikin birnin, zan yi addu'a ga Ubangiji, walƙiya kuwa za ta tsaya, ƙanƙara kuma ta daina, don ku sani duniya ta Ubangiji ce.

30. Amma dai na sani, da kai da fādawanka, har wa yau ba ku ji tsoron Ubangiji Allah ba tukuna.”

31. Rama da sha'ir suka lalace, gama sha'ir ya riga ya nuna, rama kuwa tana huda.

32. Amma alkama da maiwa ba su lalace ba, gama kakarsu ba ta yi ba tukuna.

33. Sai Musa ya fita daga wurin Fir'auna ya rabu da birnin. Ya yi addu'a ga Ubangiji sai walƙiya da ƙanƙara suka tsaya, kwararowar ruwa kuma ta ɗauke.

34. Da Fir'auna ya ga an ɗauke ruwa, da ƙanƙara, da kuma walƙiya, sai ya sāke yin zunubi, ya taurare zuciyarsa, da shi da fādawansa.

35. Zuciyar Fir'auna ta taurare, har ya ƙi sakin Isra'ilawa kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa ta bakin Musa.

Karanta cikakken babi Fit 9