Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 36:22-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Kowane katako an fiƙe bakinsa biyu don a harhaɗa su tare, haka ya yi da dukan katakan alfarwa.

23. Yadda ya yi da katakan alfarwa ke nan, ya kafa katakai ashirin a fuskar kudu.

24. Sai ya yi kwasfa arba'in da azurfa domin katakai ashirin. Kowane katako yana da kwasfa biyu saboda bakinsa biyu da aka fiƙe.

25. A fuska ta biyu ta wajen arewa ta alfarwa, ya kafa katakai ashirin.

26. Ya kuma yi kwasfa arba'in na azurfa. Kowane katako yana da kwasfa biyu.

27. Ya yi katakai shida a bayan alfarwa a fuskar yamma.

28. Ya kuma yi katakai biyu don kusurwar baya ta alfarwa.

29. Aka haɗa katakai daga ƙasa har zuwa sama inda aka haɗa su a ƙawanya ta fari, haka ya yi da su a kusurwoyin nan biyu.

30. Akwai katako takwas da kwasfansu na azurfa guda goma sha shida. Kowane katako yana da kwasfa biyu.

31. Sai ya yi sanduna na itacen ƙirya, sanduna biyar domin katakan gefe ɗaya na alfarwa,

32. sanduna biyar kuma domin katakan ɗaya gefen na alfarwa, biyar kuma domin katakan da yake baya na alfarwa wajen yamma.

33. Ya sa sandan da yake a tsakiya ya wuce daga wannan gefe zuwa wancan gefe.

34. Ya dalaye katakai da zinariya. Ya yi musu ƙawane na zinariya inda za a sarƙafa sandunan. Ya kuma dalaye sandunan da zinariya.

35. Ya kuma yi labule da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin, ya kuma yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta.

36. Ya yi wa labulen dirkoki huɗu da itacen ƙirya. Sai ya dalaye su da zinariya. Ya kuma yi musu maratayai da zinariya. Ya yi wa dirkokin nan kwasfa huɗu da azurfa.

37. Ya yi wa ƙofar alfarwa labulen da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. Ya yi wa labulen ado.

38. Ya haɗa labulen da dirkokinsa biyar, da maratayansu. Ya dalaye kawunansu da maɗauransu da zinariya, amma ya dalaye kwasfansu guda biyar da tagulla.

Karanta cikakken babi Fit 36