Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 33:11-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ta haka Ubangiji ya riƙa yin magana da Musa baki da baki, kamar yadda mutum yakan yi magana da amininsa. Sa'ad da Musa ya koma cikin zango kuma, baransa, Joshuwa, ɗan Num, saurayi, ba zai fita daga cikin alfarwar ba.

12. Musa ya ce wa Ubangiji, “Ga shi, ka faɗa mini cewa, ‘Ka fito da mutanen nan,’ amma ba ka sanar da ni wanda zai tafi tare da ni ba. Ga shi kuma, ka ce, ‘Na san ka, na san sunanka, ka kuma sami tagomashi a gare ni.’

13. Yanzu ina roƙonka idan na sami tagomashi a gare ka, ka nuna mini hanyoyinka domin in san ka, in kuma sami tagomashi a wurinka, ka kuma tuna, wannan al'umma jama'arka ce.”

14. Ubangiji kuwa ya ce, “Zan tafi tare da kai, zan kuma hutashe ka.”

15. Musa kuwa ya ce masa, “In ba za ka tafi tare da mu ba, to, kada ka ɗaga mu daga nan.

16. Yaya zan sani ko na sami tagomashi a wurinka, ni da jama'arka, in ba ka tafi tare da mu ba? Yaya ni da jama'arka, za a bambanta mu da sauran jama'ar da suke a duniya?”

17. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan yi yadda ka ce, gama ka sami tagomashi a wurina, na san ka, na kuma san sunanka.”

18. Musa kuwa ya ce, “Ina roƙonka ka nuna mini kanka.”

19. Sai Ubangiji ya ce masa, “Zan wuce a gabanka, Ni Ubangiji zan yi shelar sunana a gabanka, zan kuma yi alheri ga wanda nā yi wa alheri, in nuna jinƙai ga wanda nā yi wa jinƙai.”

20. Ya kuma ce, “Ba za ka iya ganin fuskata ba, gama mutum ba zai gan ni ba, ya rayu.”

21. Ubangiji ya ce, “Ga wani wuri kusa da ni inda za ka tsaya bisa dutsen.

22. A sa'ad da zatina yake wucewa, zan sa ka a tsaguwar dutsen, in rufe ka da hannuna har in wuce,

23. sa'an nan in ɗauke hannuna, za ka kuwa ga bayana, amma ba za ka ga fuskata ba.”

Karanta cikakken babi Fit 33