Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 29:36-46 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. A kowace rana za ka miƙa bijimi na hadaya domin zunubi ta yin kafara. Za ka tsarkake bagaden lokacin da ka yi kafara dominsa. Ka zuba masa mai, ka keɓe shi.

37. Kwana bakwai za ka ɗauka na yin kafara don bagaden, ka keɓe shi, haka kuwa bagaden zai zama mafi tsarki. Duk abin da ya taɓa bagaden zai tsarkaka.”

38. “Wannan shi ne abin da za a miƙa a bisa bagaden kullum, 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya.

39. Za a miƙa ɗan rago ɗaya da safe, ɗaya kuma da maraice.

40. Haɗe da rago na fari, za a miƙa mudun gari mai laushi garwaye da rubu'in moɗa na tataccen mai, da rubu'in moɗa na ruwan inabi domin hadaya ta sha.

41. Ɗaya ragon kuma a miƙa shi da maraice. Za a miƙa shi tare da hadaya ta gari, da hadaya ta sha kamar wadda aka yi da safe ɗin domin ta ba da ƙanshi mai daɗi, gama hadaya ce wadda aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

42. Wannan hadaya ta ƙonawa za a riƙa yinta dukan zamananku a bakin ƙofar alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji, inda ni zan sadu da kai in yi magana da kai.

43. Nan ne zan sadu da Isra'ilawa in tsarkake wurin da ɗaukakata.

44. Zan tsarkake alfarwa ta sujada da bagaden, zan kuma tsarkake Haruna da 'ya'yansa maza don su zama firistoci masu yi mini aiki.

45. Zan zauna tare da Isra'ilawa, in zama Allahnsu.

46. Za su sani ni ne Ubangiji Allahnsu wanda ya fisshe su daga Masar don in zauna tare da su. Ni ne Ubangiji Allahnsu.”

Karanta cikakken babi Fit 29