Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 29:20-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Sa'an nan ka yanka ragon, ka ɗibi jininsa ka shafa bisa leɓatun kunnen Haruna na dama, da bisa leɓatun kunnuwan 'ya'yansa maza na dama, da a kan manyan yatsotsin hannuwansu na dama, da kuma a kan manyan yatsotsin ƙafafunsu na dama. Sauran jinin kuwa, sai ka yayyafa shi a kewaye a kan bagaden.

21. Ka ɗiba daga cikin jinin da yake bisa bagaden, da man keɓewa, ka yayyafa wa Haruna da tufafinsa, da bisa 'ya'yansa maza, da tufafinsu don a tsarkake Haruna, da 'ya'yansa maza, da tufafinsu.

22. “Sai ka ɗebe kitsen ragon, ka yanke wutsiyarsa mai kitse, ka kuma ɗebe kitsen da yake rufe da kayan ciki, da dunƙulen kitsen da yake a bisa hanta, da ƙoda biyu ɗin da kitsensu, da cinyar dama, gama ragon na keɓewa ne.

23. Daga cikin kwandon abinci marar yistin da yake a gaban Ubangiji, sai ka ɗauki malmala ɗaya, da waina ɗaya da aka yi da mai, da ƙosai ɗaya.

24. Za ka sa waɗannan duka a hannun Haruna da na 'ya'yansa maza. Sai su kaɗa su domin hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji.

25. Sa'an nan za ka karɓe su daga hannunsu, ka ƙone su a bisa bagaden kamar hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Ita hadaya ce ta ƙonawa da wuta ga Ubangiji.

26. “Za ka ɗauki ƙirjin ragon da aka yanka don keɓewar Haruna, ka kaɗa shi don hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. Wannan ƙirji zai zama rabonka.

27. Za ka tsarkake ƙirji na hadaya ta kaɗawa, da cinya ta hadaya ta ɗagawa da za a kaɗa a kuma ɗaga na ragon keɓewa, wanda yake na Haruna da wanda yake na 'ya'yansa maza.

28. Wannan zai zama rabon Haruna da na 'ya'yansa maza daga wurin Isra'ilawa. Gama wannan hadaya ta ɗagawa ce daga cikin hadayu na salama da Isra'ilawa za su miƙa wa Ubangiji.

29. “Keɓaɓɓun tufafin nan na Haruna za su zama na 'ya'yansa maza bayan rasuwarsa. Da tufafin nan ne za a zuba musu mai, a keɓe su.

Karanta cikakken babi Fit 29