Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 29:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Abin da za ka yi wa Haruna da 'ya'yansa ke nan don ka keɓe su su zama firistoci masu yi mini aiki. Za ka ɗauki ɗan bijimi da raguna biyu marasa lahani,

2. da abinci marar yisti, da waina wadda aka cuɗe da mai, wadda aka yi da garin alkama mai laushi.

3. Ka sa waɗannan abu cikin kwando, sa'an nan ka kawo su cikin kwandon, ka kuma kawo ɗan bijimin da raguna biyu ɗin.

4. “Ka kawo Haruna da 'ya'yansa maza a ƙofar alfarwar ta sujada, ka yi musu wanka.

5. Sa'an nan ka kawo tufafin, ka sa wa Haruna zilaikar, da taguwar falmaran, da falmaran ɗin, da ƙyallen maƙalawa a ƙirji, sa'an nan ka ɗaura masa ɗamarar falmaran wadda aka yi mata saƙar gwaninta.

6. Za ka naɗa masa rawanin, sa'an nan ka ɗora kambi mai tsarki a bisa rawanin.

7. Ka kuma ɗauki man keɓewa, ka zuba masa a ka domin ka keɓe shi.

8. “Sa'an nan ka kawo 'ya'yansa maza, ka sa musu zilaikun.

9. Ka kuma ɗaura musu ɗamara, ka sa musu hulunan. Aikin firist kuwa zai zama nasu har abada bisa ga dokar. Haka za ka keɓe Haruna da 'ya'yansa maza.

10. “A kuma kawo bijimin a ƙofar alfarwa ta sujada. Haruna da 'ya'yansa maza za su ɗora hannuwansu a kan bijimin.

11. Za ka yanka bijimin a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada.

12. Za ka ɗibi jinin bijimin ka sa a bisa zankayen bagaden da yatsanka. Sauran jinin kuwa ka zuba a gindin bagaden.

13. Ka cire dukan kitsen da yake rufe da kayan cikin, da kitsen da yake manne da hanta, da wanda yake manne a ƙoda biyu ɗin. Ka ƙone su a bisa bagaden.

Karanta cikakken babi Fit 29