Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 19:18-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ga shi, hayaƙi ya tunnuƙe dutsen Sina'i duka, saboda Ubangiji ya sauko a bisa dutsen da wuta. Hayaƙi kuwa ya tunnuƙe, ya yi sama kamar na wurin narka ma'adinai, dutsen duka ya girgiza ƙwarai.

19. Da busar ƙaho ta ƙara tsananta, sai Musa ya yi magana, Ubangiji kuwa ya amsa masa da tsawa.

20. Ubangiji ya sauko bisa dutsen Sina'i bisa ƙwanƙolin dutsen. Ya kirawo Musa zuwa ƙwanƙolin dutsen, Musa kuwa ya hau.

21. Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, ka faɗakar da jama'ar, don kada su ƙetare kan iyakar, su zo garin a kalli Ubangiji, da yawa daga cikinsu kuwa su mutu.

22. Ko firistocin da za su kusato Ubangiji, sai su tsarkake kansu, don kada in hukunta su.”

23. Musa ya ce wa Ubangiji, “Mutanen ba za su iya hawan dutsen Sina'i ba, gama kai da kanka ka umarce mu cewa, ‘Ku sa iyaka kewaye da dutsen, ku tsarkake shi.’ ”

24. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Sauka, ka hau tare da Haruna. Amma kada ka bar firistoci da jama'a su ƙetare kan iyakar su hau zuwa wurina, don kada in hukunta su.”

Karanta cikakken babi Fit 19