Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 19:11-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Su shirya saboda rana ta uku, gama a kan rana ta uku zan sauko a bisa dutsen Sina'i a gabansu duka.

12. Sai ka yi wa jama'a iyaka kewaye da dutsen, ka faɗa musu cewa, ‘Ku yi hankali kada ku hau dutsen ko ku taɓa shi. Duk wanda ya taɓa dutsen za a kashe shi,

13. za a jajjefe shi da duwatsu ko a harbe shi da kibiya, kada kowa ya taɓa dutsen da hannu. Wannan kuwa ya shafi mutane duk da dabbobi, tilas ne a kashe su.’ Sa'ad da aka busa ƙahon rago, sai mutane su taru a gindin dutsen.”

14. Da Musa ya gangaro daga dutsen zuwa wurin mutane, ya tsarkake su. Su kuwa suka wanke tufafinsu.

15. Sai Musa ya ce musu, “Ku shirya saboda rana ta uku, kada ku kusaci mace.”

16. A safiyar rana ta uku aka yi tsawa, da walƙiyoyi, da girgije mai duhu a bisa dutsen, aka tsananta busar ƙaho, sai dukan jama'ar da suke cikin zango suka yi rawar jiki.

17. Musa kuwa ya fito da jama'a daga zango ya shugabance su, su sadu da Allah, suka tsattsaya a gindin dutsen.

18. Ga shi, hayaƙi ya tunnuƙe dutsen Sina'i duka, saboda Ubangiji ya sauko a bisa dutsen da wuta. Hayaƙi kuwa ya tunnuƙe, ya yi sama kamar na wurin narka ma'adinai, dutsen duka ya girgiza ƙwarai.

19. Da busar ƙaho ta ƙara tsananta, sai Musa ya yi magana, Ubangiji kuwa ya amsa masa da tsawa.

20. Ubangiji ya sauko bisa dutsen Sina'i bisa ƙwanƙolin dutsen. Ya kirawo Musa zuwa ƙwanƙolin dutsen, Musa kuwa ya hau.

21. Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, ka faɗakar da jama'ar, don kada su ƙetare kan iyakar, su zo garin a kalli Ubangiji, da yawa daga cikinsu kuwa su mutu.

22. Ko firistocin da za su kusato Ubangiji, sai su tsarkake kansu, don kada in hukunta su.”

Karanta cikakken babi Fit 19