Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 19:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Isra'ilawa sun kai jejin Sina'i a farkon watan uku bayan fitowarsu daga ƙasar Masar.

2. Da suka tashi daga Refidim, suka shiga jejin Sina'i, sai suka yi zango gaban dutsen.

3. Musa kuwa ya hau bisa dutsen don ya sadu da Allah.Ubangiji ya kira shi daga kan dutsen, ya ce, “Abin da za ka faɗa wa gidan Yakubu, wato Isra'ilawa ke nan,

4. ‘Kun dai ga abin da na yi da Masarawa, da yadda na ɗauke ku kamar yadda gaggafa take ɗaukar 'yan tsakinta, na kawo ku gare ni.

5. Yanzu fa, in za ku yi biyayya da ni, ku kuma kiyaye maganata, za ku zama mutanena. Dukan duniya tawa ce, amma ku za ku zama zaɓaɓɓiyar jama'ata,

6. za ku zama daular firistoci da al'umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne zantuttukan da za ka faɗa wa Isra'ilawa.”

7. Sa'an nan Musa ya je ya kira taron dattawan jama'a, ya bayyana musu dukan zantuttukan da Ubangiji ya umarce shi.

8. Dukan jama'a kuwa suka amsa masa baki ɗaya, suka ce, “Dukan abin da Ubangiji ya faɗa za mu aikata.” Musa kuwa ya mayar wa Ubangiji da amsar da jama'ar suka bayar.

9. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ga shi, ni da kaina, ina zuwa a gare ka cikin duhun girgije, domin jama'a su ji sa'ad da nake magana da kai, domin su amince da kai tutur.” Musa kuwa ya mayar wa Ubangiji da amsar da jama'ar suka bayar.

10. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je ka wurin jama'a ka tsarkake su yau da kuma gobe, su kuma wanke tufafinsu.

11. Su shirya saboda rana ta uku, gama a kan rana ta uku zan sauko a bisa dutsen Sina'i a gabansu duka.

Karanta cikakken babi Fit 19