Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 18:3-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Yetro kuma ya kawo 'ya'yanta biyu maza, Gershom da Eliyezer tare da ita. Gama Musa ya ce, “Ni baƙo ne a baƙuwar ƙasa.” Saboda haka ne ya raɗa wa ɗaya daga cikin 'ya'yansa, suna, Gershom.

4. Ya kuma ce, “Allah na ubanan shi ne ya taimake ni, ya cece ni daga takobin Fir'auna,” saboda haka ya raɗa wa ɗayan, suna, Eliyezer.

5. Sai Yetro ya kawo wa Musa 'ya'yansa maza da matarsa a cikin jeji inda suka yi zango kusa da dutsen Allah.

6. Aka faɗa wa Musa, “Ga surukinka, Yetro, yana zuwa wurinka da matarka da 'ya'yanta biyu tare da ita.”

7. Musa kuwa ya fita ya marabce shi, ya sunkuya, ya sumbace shi. Suka gaisa, suka tambayi lafiyar juna, sa'an nan suka shiga alfarwa.

8. Sai Musa ya faɗa wa surukinsa dukan abin da Ubangiji ya yi da Fir'auna da Masarawa saboda Isra'ilawa, ya kuma faɗa masa dukan wahalar da suka sha a kan hanya, da yadda Ubangiji ya cece su.

9. Yetro kuwa ya yi murna saboda alherin da Ubangiji ya yi wa Isra'ilawa da yadda ya cece su daga hannun Masarawa.

10. Yetro kuma ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya cece ku daga hannun Masarawa da Fir'auna, wanda kuma ya ceci jama'arsa daga bautar Masarawa.

11. Yanzu na sani Ubangiji yake gāba da sauran alloli duka, gama ya ceci Isra'ilawa daga tsanantawar da Masarawa suka yi musu.”

Karanta cikakken babi Fit 18