Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 16:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Taron jama'ar Isra'ila suka tashi daga Elim suka shiga jejin Sin wanda yake tsakanin Elim da Sina'i, a rana ta goma sha biyar ga watan biyu bayan fitowarsu daga ƙasar Masar.

2. Sai dukan taron jama'ar Isra'ilawa suka yi wa Musa da Haruna gunaguni cikin jejin, suka ce musu,

3. “Da ma mun mutu ta ikon Ubangiji a ƙasar Masar lokacin da muka zauna kusa da tukwanen nama, muka ci abinci muka ƙoshi. Ga shi, kun fito da mu zuwa cikin jeji don ku kashe dukan wannan taro da yunwa.”

4. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ga shi, zan sauko muku da abinci daga sama. A kowace rana jama'a za su fita su tattara abin da zai ishe su a yini, da haka zan gwada su, ko za su kiyaye maganata, ko babu.

5. A kan rana ta shida, sai su ninka abin da suka saba tattarawa na kowace rana, su shirya shi.”

6. Musa da Haruna kuwa suka ce wa Isra'ilawa, “Da yamma za ku sani Ubangiji ne ya fisshe ku daga ƙasar Masar.

7. Da safe za ku ga ɗaukakar Ubangiji, gama ya ji gunagunin da kuka yi a kansa, gama wane, mu, da za ku yi gunaguni a kanmu?”

8. Musa ya kuma ce, “Da yamma Ubangiji zai ba ku nama ku ci, da safe kuwa zai ƙosar da ku da abinci, gama Ubangiji ya riga ya ji irin gunagunin da kuka yi a kansa. Ai, gunagunin ba a kanmu yake ba, wane mu? A kan Ubangiji ne kuka yi.”

9. Musa ya ce wa Haruna, “Faɗa wa taron jama'ar Isra'ila, su matso nan a gaban Ubangiji, gama ya ji gunaguninsu.”

10. Sa'ad da Haruna yake magana da taron jama'ar, suka duba wajen jeji, sai ga ɗaukakar Ubangiji ta bayyana a cikin girgije.

Karanta cikakken babi Fit 16